Ana barazanar halaka ni – AbdulRasheed Bawa


Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin Najeriya ta’annati wato EFCC Abdulrasheed Bawa, ya ce ana ta aika masa da sakonnin barazana ga rayuwarsa tun bayan da ya hau shugabancin hukumar.
Kamar yadda BBCHAUSA na ruwaito. Ya bayyana hakan ne yayin wani shirin barka da safiya na gidan talabin ɗin Channels dake Najeriya.
”A makon da ya wuce ina New York aka kira wani babban mutum a kasar nan aka gaya masa cewa za mu halaka wannan yaron da yake shugabancin hukumar EFCC”, in ji Bawa.
Ya ƙara da cewa ”Toh ka ga wannan yana nuna maka irin yadda cin hanci ke yaƙarka a lokacin da kai kake yaƙi da shi, gaskiya ne duk inda ka waiwaya za ka ga cewa akwai matsalar nan, amma ina da kwarin guiwar cewa za mu karo karshenta a Najeriya”, a cewarsa.