Labarai
Kotu ta yanke wa matashi hukuncin bulala 15 sakamakon satar rake


Advertisment
Wata kotun shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Kwana Hudu a Jihar Kano ta bayar da umarnin a yi wa wani matashi mai suna Yakubu Haruna mai shekaru 25 bulala 15 sakamakon satar rake.
Daily Nigerian Hausa na ruwaito Tun da fari, dan sanda mai shigar da kara, Aliyu Abidin Murtala, ya shaida wa kotun cewa wani mai suna Abdullahi Muhammad, mazaunin Rimin Kebe, ya kai kara ga ofishin baturen ƴansanda da ke Zango cewa wanda ake kara ya sace masa sandunan rake guda biyu, laifin da ya saba da sashe na 133 na kundin laifuka na Penal Code na Jihar Kano.
Wanda ake tuhumar ya amsa laifin sa kuma Khadi, Nura Yusuf Ahmed, ya bayar da umarnin a yi masa bulala 15 duba da cewa wannan shi ne karo na farko da ya aikata laifin.