AddiniLabarai

Shin kungiyar Hamas dake yakar Isra’ila yan shi’a ne ? – Dr. Muhd sani umar R/lemo

A yan kwana kin nan anji wani malami ya fito yana cewa kungiyar hamas mafi yawansu yan shi’a ne inda wannan maganganu ta dauki zafi a kafafen sada zumunta inda har wasu ke cewa yace shi baya goyon bayansu tunda yan shi’a ne.

Wasu na ganin a maganganunsa babu inda ya furta baya goyon baya kawai yace mafi yawansu yan shi’a ne kuma sunce badan musulci suke yakin ba saboda kasar su ne.

Shin kungiyar Hamas da yakar Isra'ila yan shi'a ne ? - Dr. Muhd sani umar R/lemo
Shin kungiyar Hamas da yakar Isra’ila yan shi’a ne ? – Dr. Muhd sani umar R/lemo

Babba shehin malamin Dr. Sheikh Muhammad Sani Umar R/lemo yayi tsokaci akan Wannan magana a cikin wani faifan bidiyo da shafin karatutunkan malaman Musulunci sunka wallafa.

Halin da Musulmi yan yan uwan mu suke cikin a Falasɗinu tare da kisan kishiya da yahudawa suke musu tare da marawa tare da goyon bayan manyan kasashen duniya amerika da sauran ƙasashen turai muna tunatar da yan uwa ayi ta yi musu addu’a kada a kasa Allah ya dora su akansu Allah ya basu nasara akan abokan gabar su.”-inji Dr.sani

“Naga wata zanga zanga a kasar ingila harda yahudawa suna cewa allah wada ran Isra’ila, ae ansa abinda ya kawo wannan tarnaki ba mulkin malaka bane da da tarnaki, wata da nagani tana cewa hakan to a magance wannan mana.”

Shin Falasɗinawa yan shi’a ne?

 

“Duk wanda yace Falasɗinawa yan shi’a ne sakari ne baima san abinda yake ba, baima san suwaye Falasɗinawa ba, ko hamas da zaka zarga da kawance da iraq kafin su fara kawance da su sai da ko wace kasa ta labarawa sunka yi watsi da su sunka rasa wanda zasu kama.

Saboda haka a ka’ida ta musulunci duk wanda yake musulmi ko wace irin bidi’a yake inda yana faɗa da kafiri to a ka’ida ta alhussunnah indai musulmi ne indai shi musulmi ne indai baka mayar da shi kafirin ba inda shi musulmi ne ko wace irin bidi’a yake zakayi masa addu’a yayi nasara akan kafiri da yake yakarsa akan gaskiyarsa.

Ba wanda yake jayaya da cewa Falasɗinawa suke da gaskiya a rikicin da akeyi da su da yahudawa ba wanda ba wanda yake jayaya akan wannan irin yadda yan sanda Isra’ila suke galazawa mutanen Falasɗinawa su kashe su ba bakin komai ba”.- inji Dr.sani

Ga bidiyon nan domin sauraren sauran bayyanai.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button