Labarai

Yadda na ke basaja ina samo bayanai ga ‘yan bindiga ga -Wani almajiri

Wani karamin yaro wanda almajiri ne ya bayyana yadda yake samo bayanai ga ‘yan bindiga.

Almajirin mai suna Zaharaddeen Tasi’u mai shekara goma a duniya ya bayyana cewa ya fito ne daga garin Bakwai cikin jamhuriyar Nijar.labarunhausa na wallafa

Yadda na ke basaja ina samo bayanai ga ‘yan bindiga ga -Wani almajiri
Yadda na ke basaja ina samo bayanai ga ‘yan bindiga ga -Wani almajiri

Yadda yake batar da sawu yana samo bayanai ga ‘yan bindiga

Almajirin a cikin wani bidiyo da shafin Nishadi TV ya saka a Facebook, ya bayyana cewa ‘yan bindiga na turo su zuwa cikin gari domin yi musu leken asiri.

A cewar sa su kan shigo cikin gari da rana domin duba mutanen da suke da dukiya da wadanda suke da shanaye domin kai rahoton ga ‘yan bindiga a cikin daji.

Bayan sun mika rahoton leken asirin da suka yi ga ‘yan bindiga, can cikin dare sai su taho tare da ‘yan bindigan domin sace mutanen da ke da dukiya, da kuma kora shanayen zuwa cikin daji.

Almajirin ya iya amfani da bindiga

Almajirin ya bayyana cewa bai wani dade yana aiki tare da ‘yan bindigan ba, amma a dan lokacin da yayi da su har ya fara isa sarrafa bindiga.

Ya bayyana cewa da zuwan sa wurin ‘yan bindigar aka fara koya masa yadda zai yi amfani da bindiga.

Ga bidiyon a nan

Matsalar tsaro na kara tabarbarewa a kasar nan duk kuwa da kokarin da jami’an tsaro ke yi wajen ganin sun dakile matsalar tsaron.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button