Labarai

Jami’ar Gombe GSU ta karrama Dattijon da bai taba shiga aji ba, da mukamin (Dr)

Masanin ƙirkira mai kimanin shekaru 74 da bai taɓa zuwa makaranta, ya fara ƙira rediyo tun 1970

Masanin ƙirkira mai kimanin shekaru 74 da bai taɓa zuwa makaranta, ya fara ƙira rediyo tun 1970

Idan Kaji Ana Kiran Nigeria Get Talent To Da Wannan Bawan Allah Ake.

Masanin ƙirƙira ɗan kimanin shekaru Saba’in Wanda bai taɓa halartar makarantar boko ba a rayuwar shi.

Engr Hadi Usman, shine Wanda ya ƙirƙiri gidan Radio mai zaman kanshi tun wajen Shekarar Aluf da Ɗari Tara da Saba’in banda gidan Radio ya ƙirƙiri wayar salula da injin jirgi mai saukar Angulu da mashin vespa da sauran su, (Radio transmitter, Vespa engine helicopter, telephone (handset)) majiyarmu ta samu wannan labarin ta wani mutum mai amfani da kafar sada zumunta Muhammad Aminu kabir

 

Engr hadi usman

A baya bayan nan ya ƙirƙiri wani injin bada hasken wutar lantarki Wanda baya Buƙatar amfani da Man fetur domin bada hasken wutar lantarki haka ma ya ƙirƙiri Murhun Girki da yake amfani da Ruwa domin amfani dashi wajen yin girki.Jami'ar Gombe GSU ta karrama Dattijon da bai taba shiga aji ba, da mukamin (Dr) Masanin ƙirkira mai kimanin shekaru 74 da bai taɓa zuwa makaranta, ya fara ƙira rediyo tun 1970

Engr Hadi ya sauka Jami’ar jihar Gombe Inda ya gabatar da wasu fasahohin ƙirƙira da yayi yayin da ake bikin yaye ɗalibai ƴan zangon karatu na, 11th, 12th da 13th a Jami’ar ta Gombe.

Wani abun burgewa shine Injiniya bai taɓa halartar makarantar boko ba, amma dai Mahardacin Al-qur’ani mai tsarki ne tun yana Ɗan Shekaru Goma Sha Biyu 12 a duniya.

Hadi Ɗan asalin jihar Gombe ne daga yankin Jekadafari Allah ya ƙara basira Amin.

Daga karshe jami’ar jihar gombe GSU ta karrama Enr. hadi usman da muƙamin (Dr.)

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button