Labarai

Ana zargin tsohon Kwamishina a jihar Bauchi da kisan mahaifn yarinyar da yake so

Advertisment

Hukumomin tsaro a jihar Bauchi na ci gaba da tsare tsohon Kwamishina a ma’aikatar watsa Labarai ta jihar Bauchi wato Alhaji Injiniya Damina Muhammad (Galadiman Dass) a bisa zargin kisan wani bawan Allah mai suna Adamu Babanta, tsohon direba wanda ya yi ritaya a shekarar da ta gabata mai shekarun haihuwa 67 ta hanyar fisgar sa da mota yayin da yake kokarin tserewa bayan an gano yana kokarin lalata diyar mamacin. Shafin daga labaran Bauchi na ruwaito

Ana zargin tsohon Kwamishina a jihar Bauchi da kisan mahaifn yarinyar da yake so
Ana zargin tsohon Kwamishina a jihar Bauchi da kisan mahaifn yarinyar da yake so

Wakilinmu ya labarto mana cewa lamarin ya faro ne bayan da diyar mamacin mai suna Khadija Adamu Babanta ‘yar shekaru 18 da ke zaune a unguwar Yalwan Makaranta a cikin garin Bauchi ta kai korafi wa mahaifin akan cewa Injiniya Damina ya matsa yana neman lalata da ita a ranar Lahadin da ta gabata, kuma ya buga mata waya akan ta same shi a unguwar Yalwan Tudu daura da gidan mai na ATIL kusa da Jami’ar ATBU. Domin tabbatar da maganar yarinyar, sai Adamu Babanta ya bukaci yarinyar ta je ta same Injiniya Damina, inda shi kuma mahaifin ya bi ta a baya.

Cikin bayanin da Khadija Adamu Babanta ta yi wa jaridar Amana yayin da take cikin tsananin alhini da kuka, ta ce bayan da ta isa wurin da yamma gab da sallar Maghariba sai Injiniya Damina Muhammad ya bude mata kofar motarsa kana ya bukaci da ta shiga. To amma ba ta shiga ba, inda ta ce masa tana jiran mai mashin ya kawo nata sako ne, kuma ana haka ne sai mahaifin nata ya iso. A cewar ta, isowarsa ke da wuya sai ya ce masa “Galadima ni ne za ka ci amanata?” Ganin Adamu Babanta ba zato ba tsammani da kuma abubuwan da yake fada ya sa Injiniya Damina ya yi kokarin tada mota domin tserewa, yayin da shi kuma marigayi Adamu Babanta ya rike motar ta baya, sakamakon fisgar motar da Injiniya Damina ya yi, motar ta fisgi Adamu Babanta tare da hada shi da gefen kwalbati, abinda ya sa ji munanan raunuka.

Duk da an garzaya da shi asibitin koyarwa na jami’ar ATBU, malam Adamu Babanta ya riga mu gidan gaskiya. To sai dai ba yi jana’iza wa mamacin ba sai a safiyar ranar Talata sakamakon bincike da likitoci suka yi wanda rahotonsu ya tabbatar da cewa marigayin ya mutu ne sakamakon karyewan da kashin hakarkarin sa ya yi da kuma karaya biyu a kafarsa da karin wasu raunuka.

Advertisment

Wakilinmu ya ce an jibge jami’an tsaro a unguwar ta Yalwan Makaranta bayan da matsa suka fara zanga-zanga akan kisan marigayin.

Kakakin rundunar yansanda na jihar Bauchi, DSP Ahmad Wakili ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce suna tsare da wanda ake tuhuma domin gudanar da bincike.

Marigayi Adamu Babanta ya rasu ya bar mata uku da ‘yaya a kalla 20.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Check Also
Close
Back to top button