Yadda Kotu Ta Daure Lebura Saboda Ya Saci Wake Kwano 7
Wata kotu ta yanke wa wani matashin lebura hukuncin daurin wata hudu a gidan yari kan satar kwano bakwai na wake.
Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa dubun matashin mai shekara 20 ta cika ne ne bayan ya balle shagon mai kara ya sace masa kwano bakwai na Wake da manja da kiret-kiret na lemo da sauran kayan abinci.
Ya kara shaida wa kotun da ke zamanta a Jos, Jihar Filato, cewa sun gano baya ga kayan abincin, wanda ake zargin ya saci tukunyar gas da talabiji na bango da kudinsu ya kai N172,000.
Laifin,a cewarsa ya saba wa sashi na 333, da na 336, da na 273 na kundin Penal Code.
Bayan sauraron karar, kotun ta yanke wa leburan hukunci, tare da ba shi zabin biyan tarar N30,000, da kuma karin wata N30,000 din ga wanda ya yi wa satar, ko ta kara masa wata guda kan daurin.
Alkalin ya ce ya yanke hukuncin ne domin ya zamo izina ga masu aikata laifuka irin haka.
WANI LABARI: Dalilin da ya sa na cinna wa ƴaƴana biyar wuta – Dattijo mai shekara 64
Joseph Ojo, mai shekaru 64, ya bayyana dalilin da ya sa ya kona ’ya’yansa guda biyar.
Ojo, wanda aka kama shi a hedikwatar ‘yan sandan Najeriya da ke Akure, jihar Ondo, ya bayyana cewa ‘ya’yan nasa ne suka hada da mahaifiyarsu domin su yi masa duka.
Wanda ake zargin ya kuma bayyana cewa matarsa da ’ya’yan ango na cikin halin kashe shi da yunwa, duk da cewa ita ce ke bayar da kudin ciyar da shi.
A cewarsa, lamarin ya fusata shi, bayan da ya zaro mai daga chainsaw dinsa (na’urar yanka) ya zuba a dakin yaran kafin ya kona shi.
A ranar Asabar din da ta gabata ne Ojo ya banka dakin da ‘ya’yan ango ke kwana da wuta a gidansa da ke Fagun, cikin garin Ondo, hedikwatar karamar hukumar Ondo ta Yamma.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Funmi Odunlami, ta bayyana cewa uku daga cikin yaran biyar sun mutu sakamakon raunukan da suka samu a lamarin.
Odunlami ya kara da cewa Ojo ya ajiye tagwayen sa a wani daki kafin ya aiwatar da wannan aika aika