Labarai

Yadda Zaka Shawo Kan Macen A Farkon Haduwa

Wuraren shakatawa ko Sayayya wajene da mutane maza da mata suke ziyara sosai. Wajena da namiji zai iya ganin macen data masa yayi sha’awar aurenta.
Kaman yadda kowa ya sani, mata basu cika nunawa namiji suna sonshi kai tsaye kamar yadda mukayi bayani a darasin mu na baya. Don haka koda Kaine zakace kana sonta, ba nan take take amincewa sai tayi matantaka. Hakan kada ya Bata Maka rai.

Yadda Zaka Shawo Kan Macen A Farkon Haduwa
Yadda Zaka Shawo Kan Macen A Farkon Haduwa

Ga wasu dabarun na shawo kan macen da kukayi haduwan farko a irin wadannan wuraren da muka ambata a sama:

1: Yawan Kallonta- Alamun nunawa mace kana da ra’ayinta shine zuramata idanuwa.
Idan ka zura mata idanuwa kada ka dauke har sai kun hada Idanuwa da ita.
Hakan sakone dake nunawa mace kana ra’ayinta. Don haka zata yi kokarin ganin kun samu maganta idan tana ra’ayinka.
2: MaiYasa Kake Sonta: Kamin ka nunawa mace kana ra’ayinta ka tabbatar da cewa akwai wani wani dalilin daya sa kake sonta. Kada haka nan kawai ka fada son mace ba tare da wani hujja ba ko mai kankantarsa.
3: Alamu A Aikace: Bayan ka zura mata idanuwa, yi kokarin ganin cewa ka matso kusa da ita domin kokarin zantawa da ita.
Macen da ka nuna mata wannan alamar bayan zura mata idanuwa da samun dalilin sonta. Zata fahimci ka matso ne domin samun damar zantawa da ita.

4: Kada Ka Nuna Mata Zakuwarka: Sai dai kamin ka matso kusa da ita, ka tabbatar da cewa bata wanin abunda zai hanata sauraronka. Yadda zaka nuna mata zakuwar barin abunda da take domin ta saurareka.
Ka duba idan ka fahimci tana da sararin magana da kai kamin ka motso kusa da ita.
5: Ka Girmamata: Ka tabbatar lokacin da ka kusanci mace ka girmamata a lokacin da ka soma da yi mata sallama da neman izinin zantawa da ita.
Kada ka tinkari macen da kukayi haduwar farko da gadara ko isa. Girmamata zai sa ta sauke iyayin da mata suke da shi. Nuna mata gadara zai sa taki baka hadin kai…..
Zamu ci gaba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button