Labarai

Munci Amanar ‘Yan Nigeria Inji Sanata Dino Malaye

Advertisment

Daga shafin Dr Idris Ahmed (PhD Cryptology)

Tsohon Sanata Dino Malaye yace:
“Duk wanda yake rike da wani mukami na siyasa a Nigeria zababbe ne ko kuma mukamin siyasa ne, har da ni kaina (Dino Malaye) munci amanar ‘yan Nigeria..”

Dino Malaye yaci gaba da cewa; muna sayar da arzikin man fetur na Nigeria sama da shekaru 64, amma mun gaza ciyar da ‘yan-kasar Nigeria na tsawon sati biyu kacal a wannan yanayi da aka killace mutane, ba komai, Allah Ubangijin Talakawa Zai mana hisabi, ya kamata shugabanni mu tuba mu gyara”. ~Inji Sanata Dino Malaye

Dr Idris Ahmed yace; wannan shine karo na farko da na yarda da maganar Dino Malaye

Hakika ni kaina Datti Assalafiy sai naji gwiwowi na sunyi sanyi tunda har Dino Malaye ya tuba, ya kamata kowani shugaba a Nigeria ya jaddada tubarsa, mai kuskure ya gyara, wanda yake kan daidai ya kara himma, mu ma talakawa kowa ya tuba, ya gyara tsakaninsa da Allah

Muna fatan Allah Ya isar da wannan sako na Dino Malaye ga shugabannin Nigeria, Allah Ka bamu ikon tuba, Ka kawo mana mafita na alheri Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button