Labarai

Yadda Nayi Wuff Da Kyakkyawar Baturiya Cikin Kwana Huɗu Kacal -Wani Matashi

Wani matashi mai suna James Mafabi, ya bayyana yadda yayi wuff da baturiyar matar sa mai suna Gemma Bevington cikin kwana huɗu kacal bayan haɗuwar su.

James Mafabi wanda aka fi sani da Jam jim ya bayyana cewa sun haɗu da matarsa ne a wani wajen taron aure a Namakwekwe, Mbale, a Gabashin Uganda.

Yadda Nayi Wuff Da Kyakkyawar Baturiya Cikin Kwana Huɗu Kacal -Wani Matashi
Yadda Nayi Wuff Da Kyakkyawar Baturiya Cikin Kwana Huɗu Kacal -Wani Matashi

“Wata ƙawata ta nemi da in zo Uganda domin halartar shagalin bikin aurenta.” A cewar Gemma

Jaridar dimokuraɗiya ta ruwaito cewa Mafabi ya zo wajen ne a matsayin mai ɗaukar hoto da bidiyo ba tare da sanin cewa zai haɗu da rabin ran sa a wajen ba.

Du duka biyun sun bayyana cewa sun daɗe suna addu’ar samun abokan rayuwa, ba tare da sanin cewa a wannan ranar burin su zai cika ba.

“Na tuna cewa na shiga wani ɗaki na tarar da shi cike da ƴanmata na gyaran gashin su. Ina shiga idanuwa na suka yi arba da ita. A cikin zuciya ta wani abu yace min ‘itace matarka’”.

“Har cikin zuciyata ina da ƙwarin guiwar cewa tabbas watarana sai ta zama matata. Na kasance ina addu’a koda yaushe na auri baturiya sai gashi Allah ya amsa mim addu’a ta.” A cewar Mafabi.

Daga wannan haɗuwar ne suka ɗan yi hira ana cigaba da shagalin bikin, insa daga bisani ya bata lambar wayar sa.

“Bayan haɗuwar mu a wajen bikin, mun ɗauki tsawon yinin ranar muna tare. Daga nan washe gari muka tafi birnin Kampala a mota, sannan kafin ta koma Ingila a rana ta huɗu na gaya mata ina son na aure ta, inda kuma ta amince.” Inji shi.

Watanni uku bayan aukuwar hakan, suka fara shirye-shiryen auren su, wanda aka gudanar a ranar 16 ga watan Disamban 2022.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button