Labari mai daɗi: Za’a cigaba da karba tsofaffin kudi har abada – cewar CBN
Ba za a daina ƙarɓar tsofaffin kuɗi ba, cewar gwamnan babban bankin Najeriya.


Gwamnan babban bankin Nigeria CBN, Gowin Emiefele, wanda ya bayyana a gaban komitin majalisar dokokin Najeriya, ya bayyana cewar babban bankin Najeriya zasu cigaba da karɓar tsofaffin takardun kuɗi ko bayan wa’adin 10 ga watan Fabrairu.
Gwamnan babban bankin ya bayyana cewar ko bayan ƙarewar wa’adin yan Najeriya suna da damar kaisu babban bankin Najeriya domin sanya musu su cikin Asusun Ajiyar su.
A ranar Lahadi ne babban bankin ya kara wa’adin rufe karɓar tsoffin takardun Naira na 1,000 da 500 da kuma N200, biyo bayan korafin ‘yan Najeriya.
Sai dai a yayin da Emefiele ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai kan sabon tsarin sauya fasalin Naira ,da kuma canjin naira a yau Talata, shugaban na CBN ya ce har yanzu bankuna za su karbi tsoffin takardun har bayan wa’adin.
Emefiele ya ce idan aka yi la’akari da sashe na 20, karamin sashe na 3 na dokar CBN ta 2007, ko da wa’adin amfanin tsoffin kuɗaɗe ya cika, CBN za ta ci gaba da karbar su.
Emefiele ya ce dole ne bankunan kasuwanci su karbi kudin ko da bayan wa’adin 10 ga watan Fabrairu ne.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)



