“Ba Zamu Bar Kofar Shan Numfashi Wa ‘Yan Boko Haram Ba” ~Shugaba Buhari
A ziyaran da Maigirma shugaban kasar mu Nigeria Muhammadu Buhari Maigaskiya ya kai jihar Borno garin Qur’an, shugaba Buhari ya ziyarci lahiran ‘yan Boko Haram dake barikin sojoji na Maimalari Contentment a birnin Maiduguri.
Shugaba Buhari yayi dogon jawabi wa dakarun sojoji da sauran hukumomin tsaro da suke yaki da annoba ‘yan Boko Haram a karkashin rundinar OPERATION HADIN KAI, sannan ya gana da jami’an tsaron da suka samu raunuka a fagen yaki da karnukan wutar jahannama ‘yan Boko Haram.
Shugaba Buhari yace wa sojoji; nayi farin cikin kasancewa da ku yau alhamis domin na gabatar muku da bayani kan abinda ya kawoni Maiduguri, ina so na tabbatar muku da cewa har abada Gwamnatin Nigeria ba zata iya biyanku ladan aikin da kuke ba wajen sadaukar da rayukanku domin ku kare Kasarmu daga harin ‘yan ta’adda, Allah ne kadai Zai iya biya ku.
Shugaba Buhari yace, ina matukar yabawa kokarin ku, kuma ina karfafa muku gwiwa da ku cigaba da yaki cikin izza da kwazo kada ku ragarwa ‘yan Boko Haram, sannan kada ku bar wata kofa da zashu shaki numfashi, ina juyayin jami’an da suka samu shahada, ina mika sakon ta’aziyya ga ‘yan uwansu, ina mai tabbatar muku da cewa Gwamnati na zatayi kokari wajen kula da iyalan dakarun da suka rigamu gidan gaskiya a fagen yaki da Boko Haram, sannan za’a kula da lafiyar wadanda suka samu raunuka.
Ba shakka muna ganin nasaran da ake samu a yaki da ta’addanci a Arewa maso gabas karkashin Operation TURA TA KAI BANGO wanda hakan ya raunata karfin ‘yan ta’adda a tsibirin Timbuktu da jejin Sambisa da kuma bangaren sahara a yankin tafkin Chadi
A matsayina na shugaban Nigeria, kuma babban kwamandan Asakarawan tsaron Nigeria ina so na baku tabbacin cewa gwamnatina zata cigaba da fitar da kudi wajen kyautata rayuwar dakarun tsaro da sayan kayan yaki na zamani domin a isar da yaki har zuwa maboyar ‘yan ta’adda a kawo karshen su
Ina so na tunatar daku cewa akwai sauran aiki da ya kamata a aiwatar; shine a kawo karshen ta’addanci a Arewa maso gabas, a dakile ta’addanci ‘yan bindiga a Arewa masu yamma da Arewa ta tsakiya, sannan a kalubalenci sauran matsaloli na tsaro da yake addabar kasar mu Nigeria.
Don haka ku kara kwazo da kaimi domin a kawo karshen ta’addanci, dole ku kyautata neman hadin kai da sauran hukumomin tsaro na Kasarmu Nigeria, da kuma dakarun tsaro na Kasashen da suke makwabta da Nigeria Kamaru, Chadi da Niger karkashin rundinar Multinational Joint Task Force wanda suke tayamu yaki da Boko Haram, inji shugaba Buhari.
Muna fatan Allah Ya karawa shugaba Buhari lafiya da imani.
Allah muke roko Ya nuna mana karshen ta’addancin Boko Haram da masu taimakon su ta kowace irin hanya Amin,wallafar Datti Assalafy