Wani yawa malamin makaranta yankan Rago a Faransa saboda batanci ga Annabi Muhammad (SAW)
Rahotanni daga Faransa na cewa wani mahari ya kashe wani malamin makaranta kuma ya datse kansa a wani hari da ya kai a wajen birnin Paris.
‘Yan sanda sun kashe mutumin da ya kai wannan harin jim kadan bayan faruwar al’amarin, kuma muninsa ya sa shugaban kasar Emmanuel Macron halartar wurin.
Gabanin wannan harin, malamin makarantar ya nuna wa dalibansa wasu hotunan batanci na manzon Allah, Annabi Muhammad SAW.
Jim kadan bayan karfe biyar na yammacin jiya Juma’a, wani mutum dauke da wata doguwar wuka ya kai wa wani malamin tarihi hari a gaban makarantar da yake koyarwa a bayan unguwar Conflans-Saint-Honorine.
Maharin ya yi amfani da wukar wajen yanke kan malamin makarantar sannan ya tsere daga harabar makarantar, kuma ba a jima sai ya yi gaba-da-gaba da jami’an ‘yan sandan birnin.
Sai dai ya ki mika wuya su kama shi, a sanadiyyar haka ‘yan sanda suka harbe shi, kuma ya mutu a kan hanyar kai shi asibiti.
Kafofin yada labaran Faransa na cewa malamin makarantar ya nuna wa daliban da yake koyarwa wasu zane-zane na batanci da aka yi kan Annabi Muhammad SAW.
Hotunan na da alaka da harin da aka kai wa mujallar nan ta Charlie Hebdo da ta fara wallafa hotunan batancin a 2015.
Munin harin ya ja hankalin shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ya ziyarci wurin jim kadan bayan da harin ya auku.
“Ba zan yi magana kan ainihin abin takaicin da ya faru a nan ba da yammaci a Conflans Saint-Honorine, amma an kashe daya daga cikin ‘yan kasarmu saboda yana koyarwa, saboda yana sanar da dalibai ilimin ‘yancin fadin albarkacin bakinsu da kuma ‘yancin yarda ko rashin yarda. Wanda ya kai ma sa wannan harin takaicin ba abin koyi ba ne kuma harin na ta’addanci ne,” in ji shi.
Shugaba Macron ya yi kira ga ‘yan kasar da su hada kansu wuri guda.
Hutudole na ruwaito,tun farkon wannan watan wasu Musulmi kuma iyayen daliban makarantar sun kai kukansu ga hukumomin makarantar kan yadda malamin yake nuna wa dalibansa hotunan batancin a cikin ajin da yake koyarwa.
Idan aka tabbatar da cewa wannan ne dalilin da aka kashe malamin makarantar, Faransawa za su girgiza matuka — saboda a ganinsu malamin bai aikata laifin da ya wuce bayyana tarihin ainihin abin da ya auku a kasar tasu ga dalibansa ba.
Masu bincike sun tabbatar da maharin matashi ne mai shekara 18 da haihuwa kuma haifaffen kasar Rasha ne.