Tabdi Jam Wani saurayi yayiwa Budurwa Tarko kuma ta kmamata ta harda Sharin GB WhatsApp
Wani dan Najeriya ya yi amfani da daya daga cikin amfanin GB Whatsapp wajen kama budurwarsa da ke cin amanarsa.


Wani mai amfani da Twitter mai suna @only1Ayoo ya yada hirar da ya gudana tsakanin budurwar maciya amana da saurayinta, yana mai bukatan zama da kada su daina jin tsoron mata
“Baaaba, idan ka wayi gari da safen nan sannan ka daina jin tsoron mata ga tuni a nan don ka ci gaba,” @only1Ayoo ya rubuta
A hirar, budurwar mai suna Amaka ta shiryawa ainahin saurayinta mai suna Deji daddadan sako a ranar zagayowar haihuwarsa sannan ta aikawa kawarta a Whatsapp don ta duba.legit na ruwaito
Abun takaici a gareta, sai ta yi kuskuren aikawa daya saurayinta sannan ta goge sakon a lokacin da ta lura da hakan.
Godiya ga tsarin GB Whatsapp, bata iya ta goge sakon daba dukkanin bangarorin ba kuma hakan yasa daya saurayin ya gano cewa ba shi kadai ne a cikin rayuwarta ba.
Sai dai kuma ta ba da hakuri cewa sakon na wata kungiyar yan ajinsu ne, amma bai yarda ya fada a tuggun karyarta ba.
Kalli wallafar a kasa:
Omooo, If you woke up this morning and stopped fearing women here’s a reminder to continue. ???????? pic.twitter.com/MKEuHhNZOT
— PopCee! (@only1Ayoo) December 1, 2022
Jama’a sun yi martani
@Echelon26120 ya ce:
“Haka na yi gaba da sakon wata zuwa gareta dauke da taken. Dan uwa kalli wannan, zan yi wasa da hankalinta kamar yadda na saba sannan na rabu da ita idan ta fola. A takaice dai na rasa ta. Na san irin wannan kuskuren.”
@ibsudais ta ce:
“Idan haka ne me zai sa yayi fushi? wannan sakon na wanda take cin amana da shi ne amma sai ta so turawa kawarta don jin ra’ayinta a kai kafin ta tura sannan tayi kuskuren turawa saurayinta. kun gane yan zu?”
@seunney_ ya ce:
“Wasu matan dai basu da kunya.”
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




