Labarai

Bidiyon wata Amarya tana kwasar rawa a liyafar aurensu yayin da ango ya zauna takaici ya ishe shi

A wani guntun bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani an ga inda amarya ta zage a liyafar aurenta tare da kawayenta tana kwasar rawa yayin da angonta ya shiga damuwa, Shafin Arewa Fashion Style ne ya ruwaito.

Tun a bidiyon idan mutum ya kula zai ga yadda angon ya koma kan kujera ya zauna yayi tagumi da alamu duk abin duniya ne ya ishe shi. LH na wallafa

Ita kuma amaryar ta ci gaba da rawarta inda ta nuna halin ko in kula tare da kwayenta.

Mutane da dama sun yi tsokaci yayin da suke cewa ta yiwu angon yana jin haushin rawar tata ne ko kuma dai bai san zata iya wannan rawar haka ba.

Ga bidiyon a kasa:

https://fb.watch/eGr_6582k2/

Tsokacin jama’a

Labarun Hausa ta samu nasarar tattaro wasu daga cikin tsokacin mutane karkashin bidiyon:

Farfesa Bello Wakili Galadanci ya ce:

“Ango Bai so wannan show din ba zako tayi bayani da manyan baki.”

Abu Dhalib Bin Mustapha yace:

“Kunga illar Auren yar TikTok koh.”

Hizbullahi Murtala yace:

“Angon yana ta sauya tunani. Allah ya kyauta.”

Mariam Gimbiyo Oloyede tace:

“Angon yana cewa a ransa: Shin a wacce cakwakiya nasa kaina.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button