Muhimmiyar sanarwa akan Labarina Season 6 – Darakta Aminu Saira
Yanzu yanzu fitaccen mai bada umurnin a Masana’atar Kannywood ta shirya Hausa fina finai ya fitar da sanarwar akan shiri mai dogon zango wanda ake haskawa duk ranar juma’a da misalin karfe 8:30pm a tashar YouTube mai suna saira movies sai kuma tashar talabijin ta arewa24tv da misalin karfe 9:00pm.
Shine a yau din nan ya fitar da sabuwa sanarwa akan masoya masu kallon shirin Labarina zango na shidda 6 inda ya fitar da sanarwar a shafinsa na sada zumunta inda yake cewa.
“SANARWA AKAN SHIRIN #LABARINA SEASON 6.
Assalamu alaikum Masoya wannan Shiri, Kamar yadda muka sanar a karshen Episode din da ya gaba cewa mun kammala Season 5. In sha Allah 16 ga Wannan watan na December Da muke ciki, zamu cigaba da kawo muku Season 6. a wuraran da muka saba Haskawa. Muna godiya Sosai a gare ku Masoya, Allah ya bar zumunci. Allah kuma ya bamu ikon fita kunyar masu Kallo.????❤️???? Saira Movies AREWA24 #LABARINA #Labarinaseries”
Tabbas masoyan wannan shiri suna son ganin yadda zata kaya tsakanin masoyan sumayya masu son aurenta a cikin wannan fim din waye zai aureta Lukman ko Presido ko mai martaba Yerima.
A wani gefe kuma daga gidan gyaran hali yadda zata kayya tsakanin baba Dan Audu da rumfa sha shirgi.