Labarai

Babban burinta inga maza suyi mata sama da daya ayiwa mata kishiya – zainab

Matashiyar ’Yar Gwagwarmaya da Ke Fafutukar Maza Su Rinka Kara Aure a Cikin Al’umma

Najeriya – Wata matashiya ‘yar asalin jihar Adamawa mai shekaru 25, Zainab Umar ta zo da sabon salo yayin da ta bayyana fafutukar da ta dauko na wayar da kan mata su rungumi kishiya hannu biyu. Jaridar legit ta rahoto.

Babban burinta inga maza suyi mata sama da daya ayiwa mata kishiya - zainab
Babban burinta inga maza suyi mata sama da daya ayiwa mata kishiya – zainab

Zainab ta bayyana ra’ayinta, inda yace ta fahimci mata sun fi maza yawa, don haka akwai bukatar kowane namiji ya kara aure saboda kiyaye faruwar barna a waje

Ta kuma ba da kadan daga tarihin gidan da ta taso, inda tace mahaifiyarta ba ta da kishiya, amma ita dai ba za ta iya rayuwa babu abokiyar zama ba.

Ta shaidawa BBC Hausa cewa:

“Duk da cewa mamata ita kadai ce a gidanmu, amma wannan ba zai hana ni fafutukar da nake ba.”

Maza a kara aure, mata a yi hakuri a fahimta, inji Zainab

Matashiyar ta kuma yi tsokaci da cewa, ya kamata maza su kara harama, su dauki niyyar karin aure bisa gaskiya da amana tare da mutunta ta ciki da wacce za a auro.

A ra’ayin Zainab, tuni mata suka fara sauke farashi, kowacce so take a yi wuf da ita saboda yadda lamurra suka yi tsami a cikin al’umma.

A bangare guda, ta ce ita a yanzu bata da aure, kuma ba za ta iya auren wanda bai da mata ba

A kalamanta:

“Idan na samu mai mata uku zan aura, inda na samu mai mata biyu zan aura, amma dai kaddara ce za ta sa na auri wanda bai taba aure ba. Bana son na rayu bani da kishiya saboda ni ban ga aibunta ba.”

Sanannen lamari ne a duniya yadda mata ke kai makurar kaucewa hanya don ganin sun rayu babu kishiya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button