Labarai
Karin farashin mai: An bai wa Tinubu gurguwar shawara – Sanata AliNdume


Advertisment
Sanata mai wakiltar Kudancin Borno, Mohammed Ali Ndume, ya yi kira ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya duba halin da ‘yan Najeriya ke ciki tare da rage farashin man fetur da abinci.
Ndume ya ce karuwar farashin mai, abinci, kayayyaki a cikin kasar nan na yin barazana ga rayuwar ‘yan Najeriya.
A wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a a Abuja, Sanatan ya danganta halin da ake ciki da “mugayen mutane da ke yi wa gwamnatin shugaba Tinubu zagon kasa.”
Ya zargi cewa suna tura “tsauraran gyare-gyare da manufofi marasa kyau” maimakon magance matsalolin hauhawar farashi da tsadar kudin musaya.