Karin bayyani akan sabuwa kungiyar tá’áddànc! ‘Lakurawa’ da ta fito a Sokoto
Bayan wani rahoton jaridar dailytrust ta ta fitar wani dan uwa marabuci amfani da yanar gizo Shetteeman Goronyo ya yayi karin bayyani wasu sassan wuraren da wannan mutane suke da inda sunka fito da kuma yawansu da dazukan da suke
Shetteman Goronyo yayi karin haske adadin yawan su da kuma nuna hoton waɗannan mutane da labari da sunan su kawai ya fito
“Wadannan mutane sun jima a dajin Tangaza, Illela Binji, Silame Gwadabawa, da sauran wasu sassa dake a fadin wannan haujin.
Ana kiransu da Lakurawa wadanda ake kyautata zaton sun fito ne daga wajajen Aljeria.
Labari da muke samu sunfi su dubu goma zube a wadannan haujuka dajin Illela zuwa dajin Gwadabawa, zuwa dajin Tangaza, zuwa dajin Gudu da dajin da ya hada Gudu da Nijar zuwa dajin Binji da Silame duk sun kame dazuzzukan nan suna rayuwa a chiki.
Allah ne masanin abinda ake nufi damu.
Kuma shuwagabanni sunada security report da dukkan bayanan sirri akan wadannan mutane amma tsawon lokachi ba wani mataki da aka dauka domin tabbatarda kwakkwaran bincike domin sanin shin menene manufarsu ko ya al’amarin yake
Allah ya kawomana maslaha da mafita Ameen.”