Labarai

Ina Mamakin Yadda Amare suke kafaɗa da kafaɗa da Uwar Gida a wajen miji ?- Jamila Ibrahim

Shahararren yar soshiyal media Jamila Ibrahim wanda itace shugabar Home of Solace take bayyanin irin yadda wasu matan suke kishi ko gasa da uwad gida wadda kuma uwar gida itace wadda tun mijin yana ƙatulan maƙatulan suke tare amma wai yarinya na shigowa kaga tana wani irin kishi da uwar gida oh kaicho. Ga abinda Jamila Ibrahim ta wallafa a shafinta na sada zumunta

Ina Mamakin Yadda Amare suke  kafaɗa da kafaɗa  da Uwar Gida a wajen miji ba- Jamila Ibrahim
Ina Mamakin Yadda Amare suke kafaɗa da kafaɗa da Uwar Gida a wajen miji – Jamila Ibrahim
Shin Miyasa amare kuke gwagwarmayar maya da uwar gida akan miji?

 

Ina mamakin wasu amare da sukaje suka Sami uwargida da mijinta da sukayi Aure tun baida komai sannan su dinga kishi da ita Dan miji yafi kashe mata kudi…

Wasu ma harda cewa duk abunda za’awa uwargida sai dai ayi masu iri daya

Naga wacce ma tazo ta Sami uwargida da jeep tace lallai sai dai miji ya siya mata irin na uwargidan

Malama ke da kika zo jiya jiya har zakiyi graduating daga nursery ki shiga university , a Ina aka taba Hakan

Komai gradual process ne , ba’a komai da gaggawa , abunda Kai bakaso ayi Maka Kar kayiwa wani , bakisan irin gwagwarmaya da sukayi tare ba , bakisan wani irin rayuwa suka yi ba ke kinzo kin samesu kina son kiyi gasa da ita

Ba wai baya sonta ne ya auro ki ba , ba wai ya gaji da ita bane ya auro ki , ya auro ki ne Dan cika umarnin Allah da manzon sa..

Don haka kowacce Amarya ta natsu ta kama kanta har layi ya biyo ta kanta , iya biyayyar ki iya kulawa da zaki samu cikin kwanciyar hankali , ba wai gasa da rigimar zaisa ayi maki abunda kikeso ba

Da fatan an dau Wannan”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button