Labarai

Matar Aure ta rasa ranta saboda da bakin cikin an ma ta kishiya

Ash sheikh Dr. Abdullahi usman Gadon kaya a wajen majalisin karatu ya kawo wani labari mai ban al’ajabi da tausayi akan irin tsananin kishin mata.

Malam ya kawo labarin ne yadda ta kaya tsakanin alhaji da hajiya akan maganar kishiya ga yadda lamarin ya fara kamar yadda malam yake bada labari yana cewa:

” Wata mace take malam wata rana Alhaji sai kace zakayimin kishiya ko sai yace a’a ai lamari na aure Allah ne yake kaddarawa .

Idan kaji namiji yana fadar haka wallahi sai ya wallahi sai ya yanka miki kishiya komai daren dadewa ga tauhidi a wajen miji in zai ƙara aure , al’amari ne na Allah idan Allah ya ƙaddara min ba yadda na iya da ƙaddara Allah.

Sai hajiya tace duk ranar da kayimin kishiya wallahi ina jin mutuwa zanyi, amma ina sai da Allah yayi mata kishiya, ya buga ya buga ya rasa ya zai gayamata, wallahi sai bayan yaje an daura aure daga baya yaje zai gayamata.

Yaje yayi ta kewaye kewaye saboda dole ayi rabon kwana daga karshe dai yazo yace hajiya wallahi dai Allah ya kawo abun , tace me kenan arziki ka samu,yace wallahi an samu dai alkhairi , tace Alkhairi me,ya abun nan dai an samu abun, tace kayi bayyani mana yace an samar miki yar uwa .

Hajiya tace yar aiki ka kawomin ko mai, hajiya tana ta kaucewa, yace wallahi kishiya nayi miki saboda wahalhalu sunyi yawa.

Hajiya ta zabura tace aure kayi yace aure nayi tana hadiyar zuciya ta mutu a gidin kujera Allahu Akbar nan take ta fadi ta mutu . Saboda bala’in kishinku waɗanda mutane sai addu’a “.-inji Sheikh Abdallah Usman.

Dan Allah iyayenmu mata ku rage wannan tsananin kishi wanda baida fa’ida wannnan duk bala’i da tsananin abokiyar zama sanya ta rasa ranta bayan kuma Alhaji fa sai yaci amarcinsa.

Ga bidiyon nan kuji daga bakin malamin da shafin @ali_m_bukar ya wallafa.

@ali_m_bukar #ali_m_bukar #dr_abdallah_gadon_kaya #foryoupage #foryou #viral #fyp #sunnah_media #sunnahnabi ♬ original sound – Ali mustapha ✅Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button