Labarai

[Bidiyo] Ina Gargadin masu Yada hoton Amarya ta a social media – sheikh Aminu Daurawa

A daga jiya zuwa yau hoton Amarya ash sheikh Aminu Ibrahim Daurawa wanda ya karade shafukan sada zumunta sosai.

To shine gidan rediyon freedom radio fm da ke jihar kano ta samu tattaunawa da malam domin tabbatar da shin da gaske ne wannna maganar aure.

Ga yadda tattaunawar ta kasance.

[Bidiyo] Ina Gargadin masu Yada hoton Amarya ta a social media - sheikh Aminu Daurawa
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

“Ita wannan yarinya haulatu Ishaq itace gwarzuwar Kur’ani a Nigeria baki daya ita tazo na daya kuma ankayi mata kyautar wannan.

Wannan shine abinda ya bani sha’awa saboda irin kwazo da himma da wannan hafiza tayi na irin tayi kokari tazo a gaban malamai a Nigeria da ma duniya baki daya yana da kyau mu nuna kimarsu,darajarsu da kuma martabarsu.

Irin manyan malamai,attairai da sauransu ba wanda sunkayi fice a gasar kyau ba.

A cikin zantawar malam ya bada labarin wani ya bashi labarin ya auri hafizar Alkur’ani yau shekarar su ashirin da daya 21 suna da hafizan Alkur’ani guda hudu duk sun harddace Alkur’ani.

A lokaci daya tana karatun boko tana karanta macro biology tana level 300L ga hirar nan zaku iya saurarawa.

 

Malam ya kara da cewa na auri mata masu ilimi kuma naga amfanin ilimin sosai shiyasa a wajena nafi son mata masu ilimi domin darajarsu.

Wanda ana yimata kwaliya a dakin babbar ta amma wasu suje sun yada tunda ba wani taro ko biki ankayi ba duk wanda ya yada wannan ya yada ɓarna da fasadi a ban kasa.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button