Muna cikin fatara da talauci, gwamna Abba ya kawo mana agaji – Diyar Marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero
Diyar tsohon sarkin Kano, Marigayi Ado Bayero, Zainab, ta mika kukanta ga gwamnan Kano, Abba Yusuf da attajiran Kano da su kawo mata dauki ta hanyar sama musu gidan zama da kudin ciyarwa a Legas.
A tattaunawa da ta yi da PREMIUM TIMES, Zainab Ado Bayero ta ce suna cikin tsananin matsin rayuwa a halin yanzu kuma ba su da yadda za su yi, rayuwa ta yi musu tsada.
Na san mutane da yawa za su yi mamamkin a ce wai yar basarake irin Ado Bayero na wahala a duniya yanzu bayan irin dukiyar da marigayin ya rasu ya bari.
” Tun bayan rasuwar mahaifina, abubuwa suka tabarbare, yan uwana suka yi banza da ni. Ba a bani komai daga cikin gadon mahaifina ba. Suka bar mu muna ta shan wahala.
” Gida ya gagaremu, da ni da mahaifiyata da kanina. yau muna hotel a can gobe mun koma wannan. Duk da gatar da nake da shi a matsayin ‘yar tsohon sarkin Kano Ado.
Zainab ta ce ta gwamnan Kano Kabir Yusuf ya ba ta tallafi a baya amma kudin bai ishe su ba, ta ce yanzu suna bukatar akalla naira miliyan 150, sanna kuma tana bukatar a taimaka mata da kudi ta kammala wani fim da ta ke yi.
– Premium Times Hausa