Labarai

Tabdijam: An kama wata mata anan Arewa ta auri maza Uku duka babu wanda ya sani cikin mazan

Advertisment

Northern Habiscus ta bayar da labarin cewa “Na farko dai tana da shi ainahin uban yaran ta wanda sukayi auren saurayi da budurwa.
Se ta dan samu dan aikin contracts Haka ba a rasa ba a Abuja se take yawan zuwa se ALLAH ya hada ta da wani, da yai mata Fatin Aure se goganiya ta yarda.

Se take musu shift, na garin Su sati biyu na Abuja sati biyu. Duk a cikin Su ba wanda ya Sani.

Can Za tayi tafiya turai ta hadu da wani bayarabe shima yayi ta yin aure ta ce mishi ba matsala aka dada daurawa

Yanzu igiya nawa? Tara kenan ko?
Shi kenan ana nan ana nan, se ta kara haduwa da wani yai mata ta yin Aure har an fara prep se 4th husband yace Bari ya dan bincika shine fa asirin oganiya ya Tonu.

Da ran 4 ya bacci duk se da ya sannar da mazajen hajiya!!! Abu dai beyi dadi ba.

Wani labari: BAKANO YA SAKI AMARYARSA KWANA DAYA DA TAREWA

 

Wani Sabon Ango Mai Suna Jamilu A Karamar Hukumar Dawakin Tofa Dake Jihar Kano ya Saki Sabuwar Amaryarsa Mai Suna Badariyya Akan Laifin Daukar Hoton Kafin Aure (Pre wedding Pictures).

Jamilu Wanda Ya Ki Amincewa Da Manema Labarai Su Dauki Muryarsa, Ya Bayyana Cewa Tun Farko Sai Da Ya Hana Ta Yin Hoton Amma Ta Ki.

A Bangaren Amarya Badariyya, Ta Bayyana Cewa, “Ya Hana Ni Yin Hoto Tun Kafin A Daura Auren, Ni Kuma Sai Muka Yi Da Kanin Mahaifiya Ta, Shi Kuma Ya Sa Hoton A Facebook. Shine Da Ya Gani Sai Ya Sake Ni Saki Daya.”

Me Za Ku Ce Akan Wannan Abu Da Ya Faru Gare Ki?

“Ina Ba Wa Mata Shawara Su Daina Yin Abu Idan An Hana Su, Ni Yanzu Ga Abinda Ya Faru Gare Ni”.

MAJIYA: Shirin Baba Suda Na Gidan Rediyon Dala FM, Kano.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button