Labarai

2023: Gwamnonin APC sun nuna goyon bayansu ga Osinbajo

Kwanaki kaɗan bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna yanayin wanda zai gaje shi yayin da a ke tinkarar zaɓukan fidda-gwani na shugaban kasa na jam’iyyar APC, gwamnonin jam’iyya mai mulki sun fara nuna goyon baya ga mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo wanda ake ganin ya dace da irin suffar da Buharin ya bayar.

Gwamnonin jam’iyyar APC da dama ne aka hango a fadar shugaban kasa a Villa inda suka gana da Osinbajo da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, lamarin da majiyoyi ke cewa ka iya yin wani yunkuri na samun amincewar dan takarar shugaban kasa na sulhu a jam’iyyar. Daily nigerian hausa na wallafa a shafinta

Rahotanni sun ce gwamnonin da aka gani a fadar shugaban ƙasa tsakanin Laraba zuwa yau Juma’a sun hada da na Kano da Ogun da Ekiti da Gombe da Nasarawa da kuma Ebonyi.

Rahotannin sun ce da alama akasarin gwamnoni 22 da ke karkashin jam’iyya mai mulki a karkashin kungiyar Progressive Governors Forum sun amince da goyon bayan takarar Osinbajo, gabanin zaben-fidda gwani da za a fara ranar Litinin.

Rahotanni sun bayyana cewa an samu karin gwamnonin Arewa da suka hada da na Borno da Kaduna da Kano da Nasarawa da kuma Gombe da basu amince da ɗan takarar shugaban kasa da ga Arewa a karkashin jam’iyyar APC.

Gwamnonin sun gudanar da tarurruka da dama a masaukin Gwamnan Jihar Kebbi da ke Asokoro, Abuja, a ranar Talata, bayan sun gana da shugaban.

Tun da fari dai, tarurrukan da gwamnonin su ka yi ba a cimma matsaya ba a kan wadanda za su mara baya a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Sai dai kuma bayan kammala taron, rahotannin da ke fitowa daga taron sun nuna cewa gwamnonin sun amince da cewa za kai takarar shugaban kasa zuwa Kudu, inda Osinbajo yake takara.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button