Gaskiyar Labarin Cewa An Kama Mawaki 442 Tare Da Safara’u Kwana Casa’in?
Na ziyarci hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano da ke unguwar Hotoro. Mun tattauna batutuwa da dama tare da shugaban hukumar Malam Isma’il Na’abba Afakallahu wanda mutumin kirki ne mai son kawo gyara. Mun yi batun shaidanun yaran nan masu wakokin batsa wato Mr 442 da Safara’u Kwana Casa’in da kuma wakar wani Yaro mai suna Ado Gwanja Gwanja ta a sosa baya chass. Indabawa Aliyu Imam na ruwaito a shafin sa na sada zumunta.
Kafin Ado Gwanja ya saki wakar Chass hukumar tace fina-finai ta tura masa da gayyata sai ya ce yana cikin uzuri sai ya sa kafa ya tafi Ghana ya saki wakar a can. Amma Afakallahu ya tabbatar min cewa ko ba dade ko ba jima dole Gwanja ya hallara a gaban hukuma ko kuma a dauki mataki mai tsauri a kansa.
Maganar kama yaran nan Mr 442 da Safara’au ba gaskiya ba ne, ba a kama su ba, don ba sa ma Najeriya. Amma dai Malam Afakallahu ya tabbatar min cewa sun jima suna farautar yaran amma sun ki zuwa Kano. Haka nan Shugaban hukumar ta tace fina-finai ya ba ni tabbaci cewa duk wani Otal da ake hasashen suna zuwa sai da hukumarsa ta bi su a Kano don a kama su ba amma ba su zo saboda sun san idan suka zo Kano za a kama su kuma ba za su ji da dadi ba.
Ban so na yi magana kan shaidaniyar yarinyar nan Safara’u ba. Shekaranjiya ne Malam Datti Assalafiy ya kira ni cewa ya ga labarin an kama Safara’u da 442 mene gaskiyar labarin? Shi ne na kira Shugaban hukumar ta tace fina-finai ya ce min ba a kama su ba, ba ma sa Najeriya kasancewar na jima ina masa korafi a kansu sai ya ba ni damar zuwa hukumar domin tattaunawa.
Masu bibiyata idan ba su manta ba tun a shekarar 2020 sanda bidiyon tsiraicin wannan shaidaniyar yarinya ya fita, na kai karar ta hukumar Hisba da hukumar tace fina-finai. A lokacin ne Afakallahu ya tabbatar min cewa za a kore daga Fim. Za ku iya karanta rubutun na wancan lokacin ta hanyar shiga link din da ke kasa..
Bayan nan Malam Afakallahu ya tabbatar da maganarsa, don wata rana ya kira ni ya tabbatar cewa hatta a shirin kwana casa’in an cire ta. Na yi posting a lokacin kan haka za ku iya ganinsa ta hanyar shiga link din da ke kasa.
Masu cewa wai ba a yi daidai don an kori Safara’u daga Fim, ke nan ita abin da ta yi daidai ne? A Najeriya kasar da ba a kan doron addini take ba hukumar ‘yan sanda ta kori wata Mace saboda ta yi cikin shege. Kwanan nan ba da jimawa ba hukumar ta ‘yan sanda ta dauki mataki kan wasu mata biyu da suka je yawon shakatawa suka dauki hoto wanda ke fitar da cinyarsu da cibiyarsu. Ita Safara’u bidiyon batsa ta yi wato “Blue Film” babu inda ba a gani a jikinta ba. Ai babban adalci aka yi mata da hukuncin ya tsaya a kora daga fim, don hakan shi ne daidai kuma ya zama darasi da izina. A kundin doka na hukumar tace fina-finai mai suna “Censorship Regulation” Sashi na 98 karamin sashin (C) na cikin baka cewa ya yi a daure Safara’u wata uku a ci tarar ta kan laifin da ta yi. Bayan nan kundin Shari’a na Arewa wato ‘Penal Code’ Sashi na 407 cewa ya yi a daure Safara’u Shekara d’aya kuma a ci tarar ta. Wanda mun yi ta kokari don ganin Hisbah ta kama ta ta gurfanar da ita a Kotu amma aka ki yi saboda ba addini ne a gaban shugabannin ba.
BBC Hausa jaridar Yahudawa ‘yan kwangila makiya musulunci har da nemo yarinyar nan su yi Hira da ita don su kamBBC Hausau nuna wa jama’a iskancin da take ma daukaka taBBC Hausaka kwanaki fa suka yi ta Kambama wani dan iskan Yaro da ya shirya Fim din koyar da Jima’i suna hira da shi don wasu ma su kwaikwaiya a yi hira da su duniya ta san su. Shahara kan aikata iskanci aikin banza ne, Safara’u da girmanta da hankalinta idan P*rnography ‘Blue Film’ za ta yi ta je ta yi ai kanta take yi wa za ta girbi abin da ta shuka, duniya daidai take da ita don ta koya wa ire-irenta darasi. Kuma karya take da ta ce wai ta yi bidiyon ne ta ajiye a wayarta, me ta fada wa Afakallahu? Afakallau ya fad’a min, ita ta ce masa Saurayinta ta yi wa kuma ta tura masa, karya kuma take da ta ce wai kashi saba’in na mata na yin bidiyon tsiraicinsu su ajiye a wayarsu. Amfanin me hakan zai musu? Wani ya gani ya yada duniya ta gani? Babu mai hankali da tunanin da za ta yi haka. Da Safara’u na da hankali bayan fitar bidiyonta sai ta tuba ta yi aure kamar yadda Maryam Hiyana ta yi. Amma ba komai ga ta nan ga duniya nan.
Muna addu’a Allah ya shirye ta da ire-irenta.