Kannywood

Abin da ya sa jaruman Kannywood na yanzu ba su yin ƙarko – Auwalu West

FITACCEN jarumin Kannywood, Auwalu Isa (West), ya bayyana dalilin da ya ‘yan wasan fim na yanzu ba su daɗewa a tashe, da sun fito an san su sai a ji su shiru.

A cewar sa, jaruman da ake da su yanzu ba su girmama na gaba da su, kuma hakan ne ya sa ba su da wani tasiri. Jaridar fimmagazine na wallafa

A tattaunawar da ya yi da mujallar Fim dangane da yadda harkar fim ta ke a da da kuma yanzu, West ya ce: “A gaskiya yanzu jarumai mazan su da matan su ba kamar yadda mu ka yi a baya ba ne, lokacin da mu ka shigo harkar.

“A wancan lokacin duk wani babba ana yi masa biyayya, kuma ana tsayawa a koyi aikin sosai don a ƙware, wanda a yanzu ba haka ba ne.

“A yanzu duk wanda ya zo so ya ke lokaci kaɗan ya yi suna, duniya ta san da shi. Kuma a irin wannan sai ka ga ko da an yi sunan na lokaci kaɗan ne, ka ji an daina maganar mutum.

“Amma mu na baya da mu ka tsaya mu ka sha wahala mu ka yi aikin har yanzu fuskar mu ba a manta da ita ba. Yanzu sai ka ga jarumi ya yi finafinai da yawa, ya yi waƙoƙi, amma ba a san shi ba, sai ka ga ma idan zai je wani wajen sai ya neme mu mun shige masa gaba, don ba a san shi ba.”

Abin da ya sa jaruman Kannywood na yanzu ba su yin ƙarko – Auwalu West
Auwalu Isa West: Mu girmama manyan mu

Jarumin ya ƙara da cewa: “Ƙoƙarin a yi suna cikin sauri ne duk ya sa jaruman yanzu ba su da daraja, kuma ba sa yin dogon zamani. Amma mu da yake mun tsaya an koya mana  kuma mun san darajar manyan mu, shi ya sa mu ka kawo yanzu ana damawa da mu.

“Kuma alhamdu lillahi a yanzu harkar fim ta zama rufin asiri a gare ni, don ita ce ta fito da ni duniya ta san ni har na samu abin da na samu da har ma wasu su ke samu daga waje na.”

Karanta kuma  Hotuna: Taron ƙaddamar da AKAFA

West ya yi kira ga ‘yan fim da “su sani lokaci ya yi da za mu haɗa kai da kuma girmama manyan mu, saboda mu ceto masana’antar daga yanayin da ta ke ciki a yanzu.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button