Kannywood

RASUWAR MAHAIFIN ALI NUHU: Ya Kamata Mu Yi Wa Ali Nuhu Kara A Matsayinsa Na Dan Uwanmu Musulmi

Advertisment

…jan hankali ga masu kalaman batanci kan mutuwar

Daga Salisu Magaji Fandalla’fih

Jiya ne Allah ya yi wa mahaifin jarumi Ali Nuhu mai suna Nuhu Poloma tsohon dan majalisa kuma tsohon shugaban PDP a Gombe rasuwa.

Game da cewa shi wannan mutum mahaifin na Ali Nuhu Kirista ne hakan ya sa wasu ke ta fadar maganganu mara dadi. Ba a ce ku yi masa addu’a ba tunda ba musulmi bane amma dan Allah ko don nuna kara ga Ali Nuhu ku bar aibata shi ko zage-zage.

A tunani na abin farin ciki ne uba wanda ba musulmi da dansa Musulmi ma’ana har uban ya gama abinsa bai ja hankalin dansa ya bi shi ba dan ya tsaya kan addinin sa bai dubi dukiyar mahaifinsa ba sai ya tsaya da kafarsa kuma bai yarda mahaifinsa ya ja ra’ayinsa zuwa wani addinin ba.

Ali Nuhu musulmi ne dan haka mu nuna kara ga dan uwanmu musulmi mu daina fadar maganganu kan mahaifinsa, ku duba da kyau har yanzu Ali Nuhu bai bayyana rasuwar mahaifin nasa ba, kuma ina kyautata zaton maganganu marasa dadi yake gudu.

Ali Nuhu musulmi ne dan Allah mu daina, kokuwa so ake a cusawa masu son musulunta kin addinin, kada fa ku manta koda mutum yana musulmi mahaifinsa na Kirista yana sonshi na matsayin mahai fi.

Idan kuwa har mukaci gaba da haka tsoron kada ajefi mutum da maganganu idan mahaifinsa ya rasu na iya sa kirista yaji tsoron musulunta, Dan Allah mu kiyaye.

Allah ya baiwa Ali Nuhu hakurin jure wannan rashi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button