Labarai

Yadda matashi ya halaka mahaifinsa kan rikicin gona a Nasarawa

Advertisment

Mutanen garin Masaka a cikin ƙaramar hukumar Karu ta jihar Nasarawa a ranar Litinin, sun shiga cikin ruɗani da tashin hankali bayan wani matashi ɗan fari Tunde Badejo ya halaka mahaifinsa Badejo Idowu saboda taƙaddama akan gona wacce mallakar iyalan gidan ce. Shafin LH ya wallafa Yadda matashi ya halaka mahaifinsa kan rikicin gona a Nasarawa

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Tunde ya addabi mahaifin na sa kan ya mallaka mishi wani yankin ƙasar gonan tun sama da shekara ɗaya nan baya.

An bayyana yadda matashin ya aikata wannan ɗanyen aikin

Matar mamacin, Madam Tolani Badejo, ta shaida wa wakilin jaridar yayin da ya ziyarci wurin da abun ya faru cewa mijinta ya roƙi Tunde ya ba shi lokaci domin raba gonar cikin adalci ga dukkan iyalan gidan.

Madam Tolani ta ce:

Tun shekarar da ta gabata yake damun mijina kan maganar gonar, to a ranar Litinin lokacin da suka samu saɓani na ƙarshe, sai ya zaro wuƙa ya daɓa wa mahaifinsa a wurare daban-daban.

Ya daɓa masa wuƙa a kai, wuya, ƙirji, hannuwa da ƙafafu har sai da ya halaka shi. Na nemi ɗauki amma tuni ya tsere.

An miƙa lamarin zuwa ga hukumar ƴan sanda

Ayomide Badejo, ɗa na biyu ga mamacin, ya bayyana cewa tuni suka miƙa rahoton lamarin da ya auku ga hukumar ƴan sanda yayin da aka kai gawar mahaifin su ɗakin ajiyar gawarwaki.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button