Labarai

Buhari ya ce ‘yan bindiga na son kure hakurin da yake yi da su

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gargadi ‘yan bindigar da ke kashe-kashe musamman a arewacin kasar kan cewa “Su shiga hayyacinsu, su daina jin cewa gwamnati ba za ta iya maganinsu ba”.
Kamar yadda Bbchausa na ruwaito.Buhari ya yi wannan gargadin ne a ranar Alhamis yayin da yake Allah-wadai da kisan da ‘yan bindigar suka yi wa mutane sama da 50 a kauyukan Zamfara.
Shugaban wanda ya yi gargadin cewa “Za a kawo karshen Irin wannan rashin girmama rayuwar mutanen da ‘yan bindigar ke yi a kusa ba da dadewa ba”, ya kara da cewa, “Dole mu dakatar da wannan kisan da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba”,
Shugaba Buhari ya tabbatarwa da al’ummar jihar Zamfara cewa “duk da gazawar da muka yi a kokarinmu na kare ‘yan kasarmu, ba za mu taba bayar da kai bori ya hau ba wajen murkushe wadannan marassa tausayin.”
Buhari ya yi alkawarin kaddamar da wani shirin soji na musamman a Zamfara domin “dakile hare-haren ‘yan bingidar” da kullum ke kamari.
“Gwamnatinmu ba za ta yarda da kai kashe ‘yan kauyen da ke talakawa ba suke fama da talauci da sauran matsalolin rayuwa,” in ji Buhari a wata sanarwa da kakainsa ya fitar Garba Shehu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button