Uncategorized

ALLAH SARKI: Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Miji Da Matarsa, Wadanda Dukkansu Likitoci Ne (Hotuna)

Waɗannan ma’auratan, sun kasance likitoci, kuma suna aiki ne a asibitin UMTH dake Maiduguri jihar Borno. Sun rasu ne bayan da gobara ta kama gidansu.ALLAH SARKI: Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Miji Da Matarsa, Wadanda Dukkansu Likitoci Ne (Hotuna)

ALLAH SARKI: Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Miji Da Matarsa, Wadanda Dukkansu Likitoci Ne (Hotuna) ALLAH SARKI: Gobara Ta Yi Sanadiyyar Mutuwar Miji Da Matarsa, Wadanda Dukkansu Likitoci Ne (Hotuna)

 

Da farko mijin mai suna Dr Auta ne ya fara mutuwa, washegarin safiyar ranar Laraba ita ma matar, Dr Amina ta rasu.

Majiyar ta bayyana cewa an binne marigayi Dr Auta Gidado daidai da koyarwar musulunci bayan an sallaci gawarsa a masallacin UMTH.

Majiyar ta ci gaba da cewa: “Kasa da sao’i 24 bayan mutuwar mijin, mun kuma rasa Dr Amina Ahmad a safiyar yau (jiya). Mun samu sakon da misalin karfe 3:00am.

Yayin da yake tabbatar da lamarin, Shugaban kungiyar likitocin UMTH, Dr Abdullahi Usman, ya nuna bakin ciki kan mutuwar ma’auratan.

Ya ce: “Eh mun rasa su su biyun sakamakon gobara. Yanzu haka da muke magana, babu wanda zai iya baku cikakken bayani, amma abun da aka fada mana shine cewa gobarar ta barke ne daga fetur.”

Ya kara da cewa: “Ina fatan mutane za su mutunta mamatan. Wannan lokacin bakin ciki ne a garemu mu

Allah ya jiƙan su da rahama.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button