Labarai

Nayi bakin cikin mutuwar Sheikh Abubakar Giro – Atiku Abubakar

Mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP ya wallafa irin yadda yaji radadi da jimamin mutuwar babban shehin malamin addinin Muslunci da ke arewacin Najeriya Sheikh Atiku Abubakar inda ya wallafa wannan sanarwa a shafinsa na sada zumunta facebook.

Ga abinda yake Cewa :

Na shiga jimami da bakin cikin jin labarin rasuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu, babban malamin addinin musulunci bayan gajeruwar jinya a jihar Kebbi.

Sheikh Abubakar Giro Argungu ya samu karramawa sosai a tsakanin malamai da sauran jama’a saboda irin gudunmawar da yake bayarwa ga addinin Musulunci a Najeriya a matsayinsa na daya daga cikin manyan malaman Najeriya da Afrika.”

Babban shehin malamin yayi shekara 45 yana karantawa wanda tabbas malam ya dade yana yiwa addini hidima anyi jana’izar Sheikh Abubakar Giro Argungu Rahimahullah a yau alhamis da misalin karfe 2:30pm a cikin garin argungu inda manya manyan malaman addinin musulunci sun halarci jana’izar Sheikh malamain.

Sanarwa ta cigaba da cewa:

Tabbas koyarwarsa da ka’idarsa ta zaman lafiya da haɗin kai kasa za su cigaba da amfanar al’uma.

A Madadin Iyalina, Ina Mika Ta’aziyyata Ga Iyalan Gidansa, Da Al’ummar Musulmi Da ‘Yan Nijeriya Baki Daya. – Allah ya jikan Malam ya gafarta masa. Ameen. – AA”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button