Labarai

Yadda mulkin Bola Tinubu Zai kasance – Masanin Siyasa a Nijeriya

Advertisment

Idan Allah ya kudirta Asiwaju Ahmed Bolawale Tinubu ya ci zabe a 2023, to ga yadda mulkin sa zai kasan ce.

Da farko zai zabo zakakuran kwararrun mutane wadanda zasu taya shi gudanar da sha’anin mulki, kamar yadda yayi lokacin yana gwamnan legas.

zai sa a fito masa da matsalolin Nigeria, ya yi ma su kalon tsanaki daganan sai a fara wasa a take ball.

A wajen nadin ministoci anan za a fara gane mecece agendar Tinubu. domin a take zai dauki ministocin Aiyuka, Kudi, sharia, sufuri, wuta, da Abuja harkokin cikin gida , zai ba yankin sa na kudu maso yamma.

Advertisment

zai dauki Ministocin tsaro, da yan sanda da kwadago, da jin kai , da yada labarai ya kawo Arewa, saboda ya san babu wani tasirin da zasu iya yi, ko kawo wa Arewa ci gaba.

sannan zai Dauki kamar na lafiya, kimiya da ilimi ya kai kudu maso gabas, mai da harkokin waje kudu maso kudu.

A ma’aikatu kuwa zai dau FIRS, NPA, DSS, NCC, AGF, CUSTOM, POLICE, DIA, DMI, NIA da sauran muhimman Parastatal ya bai wa yarbawa kamar yadda Buhari yayi, sai dai bambancin su ,shi ne kowannen su za ba shi aikin da zai yi, tun daga daukar yan kabilar yarbawa aiki zuwa gina yankin yarbawa.

Aiki na farko da zai fara Sa wa hannu ya ba da kudin yin sa da gaggawa shine sada jihohin yarba da hanyar dogo ta zamani wato Railways.

sannan zai yi kokarin samar da wutar lantarki ta kowacce hanya, ga kasashen yarbawa kamar Obasanjo ya yi diverting National grid zuwa ogun don bunkasa masana’ntu.

sannan zai samar da kyakkyawan tsaro a jihohin yarbawa bayan ya samar da wuta, sai ya kwadaitar da masu sanya hannun jari na kasashen waje su zuba jari su gina masana’antu.

Zai din ga ba wa dattawan Arewa da manyan Arewa kwangiloli wanda ba zasu iya karasawa ba, daga karshe su cinye kudin.

zai cire tallafin mai saboda lokacin matatar man Dangote za ta fara aiki, amma kafin nan zai tabbatar ya hada bututun mai zuwa jihohin yarbawa. yan Arewa dole su dinga dakon sa a mayan motoci anan farashi zai bambanta.

daga nan zai bude boda ya cire takunkumin shigo da shinkafa, kamfanonin Arewa da manoma za su karye.

sannan duk tashoshin tsaundari irin su NEPZA zai hana su aiki sai dai ka dau kaya ko ka dora a legas.

Idan majalisa ta ba shi dama zai kirkiri state police, idan kuma bata ba shi dama zai karfafa Amotekun har su fi NPF tasiri.

daga nan zai farfado da OPC, zai karbo Sunday igboho, ya bashi kwangiloli, duk lokacin da yan Arewa suka yi Barazana sai ya sa shi ya tayar da harkar yoruba nation.

Dan Arewa kuma zai ta ganin wulakanci iri iri a legas, mussaman manyan motoci masu dakon kaya daga legas zuwa Arewa, Area boyz za su dinga chajin su kudi kala kala.

zai Rage kudin aikin Hajji don ya daddawa yan Arewa rai.

zai dawo da AlmaJiri schools don ya nuna kaunar Arewa, yayin da zai ta tura yarbawa karatu a waje akan tsarin scholarship.

zai koro fulani daga jihohin yarbawa zuwa Arewa, kuma ta’addanci zai iya karuwa a arewa.

Zai kasance babu ruwan sa da addini walau na musulinci ko na kiristanci. amma matarshi tunda pastorce za ta taimakawa kiristoci a inda suke bukata.

Sannan zai sakar wa magoya bayanshi musamman yan Arewa kudi masu nauyi da kwngiloli domin kare manufofinsa.

daga karshe zai yi Re-structuring.

Aminu Hassan
political scientist
10062022

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button