Musulman Inyamurai Zasu Ƙaddamar Da Alƙur’anin Da Suka Fassara Da Inyamuran Ci
Kungiyar musulmin yankin Kudu maso Gabashin kasar nan za ta kaddamar da kur’ani mai tsarki da aka fassara zuwa harshen Igbo, a ranar juma’a mai zuwa.
Wakilan kungiyar da ke karkashin kungiyar Da’awah Muslim Ibo karkashin jagorancin Mal. Muhammed Muritala Chukwuemeka ya bayyana hakan ne a jiya a yayin wata ziyarar ban girma da ya kai ofishin Family Trust a Abuja. Jaridar Jakadiya na ruwaito
Da yake jawabi yayin ziyarar, Mal. Chukwuemeka ya ce shi da tawagarsa sun yanke shawarar isar da sakon Allah ga ‘yan’uwansu Igbo ta hanyar Kur’ani da aka fassara.
Malam Chukwuemeka, dan asalin karamar hukumar Orlu ta jihar Imo, ya bayyana addinin musulunci a matsayin addinin zaman lafiya da ya haramta kashe mutane.
Ya bayyana cewa ya kwashe shekaru biyar masu kyau kafin ya kammala fassarar.
Limamin dan asalin Imo, ya yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishi da su halarci kaddamar da taron da za a yi bayan sallar Juma’a a masallacin Ansar-ud-deen da ke Maitama, Abuja.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya masu kishin kasa da su tallafa wajen samar da littafi mai tsarki domin isar da sakon Allah cikin kwanciyar hankali ga ‘yan kabilar Igbo da ke Kudu maso Gabas da sauran sassan Najeriya.
“Ba a kai shekara biyar ba kafin na kammala fassarar. Muna kira ga ’yan Najeriya masu hannu da shuni da su taimaka wajen samar da littafi mai tsarki da yawa. A yanzu haka mun buga kwafi 500 kuma an riga an tura kwafi 100 zuwa Kudu maso Gabas,” inji shi.