Wani Saurayi Ya Yada Hotunan Tsiraicin Wacce Zai Aura Saboda Kishi
Lallai kishi yanzu yabar mata ya koma ga maza kamar irin yadda wannan labarin zai baka mamaki ta yadda wannan saurayi ya haɗa hoton tsirancin budurwarsa duk a cikin kishin da yake mata kamar yadda Tonga Abdul Tonga ya wallafa
Ina ‘yan matan da suke rawan kan turawa samarinsu hotuna da bidiyo na tsairaicinsu. To kuyi hattara ganin yadda irin wadannan samarin naku basu da kangadon lissafi.
Yanzu haka dai wata budurwa da wani saurayin da yace yana sonta da aure ya kassara mata rayuwa ganin yadda ya tura hotunan tsiraicinta a kafafen sada zumunta domin kawai yana kishin ganinta da wani saurayin.
Budurwa wacce ‘yar jami’a ce ance ta shiga tashin hankali matuka bayan da ita da kanta ta soma ganin hotunan kamin na kusa da ita su soma kiranta suna Allah wadai da ita.
Sai dai saboda munin wadannan bidiyon da hotunan da kuma mutunta wannan diyar yasa baza mu sako hotunan da bidiyon ba.
Da wannan ne muke jan hankalin ‘yan mata musamman masu soyayya da samarin nan masu taka wando da su kiyaye tura musu hotunan tsairiaci da yanzu haka ya zama abun kwalliya ga masoya gudun kada wata rana ya nuna miki wauta da yarinta.