Mr 442 Yayi Martani Mai Zafi Ga Yan KannyWood
Mawaki Mr 442 Yayi Zazzafar Martani Ga Yan KannyWood Kan Maganar Da Safara’u Take Cewa “Na Canja Gida” Na Canja Kala” Na Bar Sanar Wa Yan Wahala” Matashin Mawakin Dai Shine Ubangida Ga Wannan Mawakiyar Safiya Yusuf Wacce Akafi Sani Da SAFAA.
Inda Ya Fito Ya Zama Garkuwa Ga Mawakiyar, Ya Bayyana Cewa Tunda SAFAA, Ta Nemi Sulhu Da Yan KannyWood Kuma Ta Basu Hakuru Amma Kuma Sunki Yarda Da Abin Da Ita, Kuma Sunki Amincewa Akan Ayi Sulhu Kam Maganar Da Take Fadi Akansu.
Yace Duk Matakin Da Zasu Dauka To Suje Su Dauka Shima Daga Karshe Ya Maimaita Wannan Baitin Nata Na Cewa “Ta Canja Gida” Ta Canja Kala” Tabar Sana’ar Wa Yan Wahala.
Ga Yadda Mawakin Ke Bayani Da Bakinsa.
https://m.youtube.com/watch?v=B3JWQlrtIaU&feature=youtu.be
Via Hausamini