Kannywood

Abin farin cikin da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne ranar mutuwar mahaifiyata, – Cewar Momi Gombe

Jarumar Kannywood, Maimuna Abubakar wacce aka fi sani da Momi Gombe ta ce ranar da ta fi ko wacce rana farinciki a rayuwarta da kuma bakinciki ita ce ranar da mahaifiyarta ta kwanta dama.

Ta bayyana hakan ne a shirin BBC Hausa mai suna Daga Bakin Mai Ita. A ranar 31 ga watan Maris din 2022 ne BBC Hausa ta wallafa bidiyon tattaunar da ta yi da jarumar.

Da farko ta fara da gabatar da kanta inda ta ce ta yi firamare da sakandare a garin Gombe. Sannan duk rayuwarta a cikin garin ta yi, sai yanzu kuma sana’a ta mayar da ita garin Kano.labarunhausa na tattaro labarin

Ta bayyana yadda ta fara fim

Ta shaida yadda ta shiga fim ta hannun wani mai gidanta Usman Mu’azu, kuma dan garinsu ne sannan ya saba da ‘yan uwanta.

Ta ce idan ‘yan fim suna aiki yana burgeta hakan yasa idan aka aiketa kai musu abinci take tsayawa ta dinga kallonsu. Daga nan ya sanyata a shirin.

Ta ce ya tuntubi mahaifiyarta daga nan ta amince inda aka sanyata ta fara shirin fim. Ta ce tana matukar farinciki da alfahari da wakar Jarumar mata wacce suka yi bidiyon da Hamisu Breaker.

Ta ce babu wata soyayya da ke tsakaninta da Mawaki Breaker, kawai mutane ne suka fadin hakan.

Sunusi Oscar 442 ne mai gidanta nan a Kannywood kuma babanta, sannan shi ne darektan da ta fi so.

Ranar mutuwar mahaifiyarta ce ranar farin ciki da bakin cikinta

Yayin da aka tambayeta abinda ya ke sata farinciki sai ta kada baki ta ce:

Abinda ya ke sa ni farinciki shi ne ibadata. Duk lokacin da na ji ina ibada, ina samun farinciki.”

Abinda ya ke sa ta bakin ciki shi ne idan ta tuna mutuwar mahaifiyarta.”

Ta kara da cewa:

Abin farincikin da ba zan iya mantawa da shi ba shi ne ranar da mamata ta rasu. Rabuwata da ita ta karshe shi ne ranar bakincikina kuma ranar farincikina.”

An tambayeta dalilin da yasa ta yi farinciki a ranar da mahaifiyarta ta mutu shi ne ta ce:

Abinda yasa na ke farinciki shi ne ni ce wacce na yi maganar karshe da ita kaf a cikin ‘yan uwana. Kuma ni kadai nasan irin maganganun da muka yi da ita da irin addu’o’in da ta yi min.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button