Kannywood

Matsayin da na ba mahaifina na gida, shi na bai wa Adam Zango -Jaruma Tumba Gwaska

Advertisment

Bayan wani gidan talabijin na FarinWata ya yi hira da jaruma Tumba Gwaska, an tambayeta akan yadda take da alaka mai karfi tsakaninta da Jarumi Adam A. Zango har wasu suke ganin kamar soyayya ce tsakaninsu, kamar yadda Tashar Tsakar Gida ta ruwaito.

Labarunhausa ta wallafa Sai dai a bayaninta, ta tabbatar da cewa babu soyayya tsakaninsu, Uban gidanta ne shi sannan matsayin uba yake a wurinta kuma akan shi sai inda karfinta ya kare.

Kamar yadda ta ce:

“To a gaskiya dai babu komai tsakanina da Baba Ado, Wallahi Wallahi babu komai tsakanina da Adamu sai mutunci. Yadda na dauki girma na ba mahaifina na gida, haka na dauka na ba Adam.

Advertisment

“Uban gidana ne shi, ina ji da shi, ina alfahari da shi kuma sai inda karfina ya kare akanshi saboda ai dan halak shi ake yi wa halacci inji bahaushe.”

Yayin da aka tabo ma Tumba batun Safara’u wanda tace musu ‘yan wahala, ta ce kowa yayi nagari don kansa.

Ta ce fim ne ya sanya Safara’u yin suna sannan babu yadda za ayi mutane su kalleta idan banda fim din da ya fito da ita.

Tumba ta ce korar Safara’u da aka yi daga fim shi ne ya bata mata rai har ta dauka zafi take caccakar sana’arsu.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button