Labarai

Su A Borno Talakawa Ake Bawai Kayan Abincin Azumi Ba Exco Ba

Gwamna Zulum ya fara ziyarar watan Ramadan daga ƙaramar hukumar Mafa; Inda ya raba tsabar kuɗi Naira Milyan Saba’in da Shidda N76m kazalika kuma aka bada kayan Abinci ga Mutane Dubu Goma Sha Biyar da Ɗari Ukku da Ashirin da Bakwai 15,327.
Gwamna Babagana Umara Zulum, a Yau Asabar ya fara Azumi ne daga ƙauyen su Mafa, jihar Borno Inda ya ƙwana garin jiya Juma’a da Safiyar Yau Kuma ya fara rabon kayan Azumi.

Su A Borno Talakawa Ake Bawai Kayan Abincin Azumi Ba Exco Ba
Su A Borno Talakawa Ake Bawai Kayan Abincin Azumi Ba Exco Ba

Adadin waɗanda aka rabama kayan sun haɗa da Mata Dubu Tara da Ɗari Ukku da Goma Sha Ukku 9,313 da Maza Dubu Shidda da Goma Sha Hudu 6,014 kowannen su ya samu Naira Dubu Biyar N5,000 kuɗin da suka tashi N76,635,000:00.
Bayan kuɗin kuma kowane Namiji ya samu Buhun Shinkafa mai nauyin 50kg da kuma yadin Shadda Biyar, yayinda Matan kuma kowace ta samu buhun Suga Mai nauyin 10kg da turmin Atamfa.
Nidai nace tunda Exco ake baiwa a Garin mu, Al-ummar Gari ranar ku na zuwa Idan lokacin zaɓe yayi sukazo wajen ku neman ƙuri’a ku turasu wajen Exco.”
Daga : Muhammad Aminu Kabir

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button