Labarai

Rikicin Masarautar Kano: Wurare 5 Da Sabon Kudirin Gwamna Ganduje Zai Shafi Sarkin Kano

Bayan kotu ta wargaje Masarautun kasar Bichi, Karaye, Rano da Gaya da gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kafa. Gwamnatin Kano ta sake dawo da maganar ta hannun majalisar dokokin jihar.
Jaridar Sauraniya a shafin Facebook ta ruwaito.

Daily Nigerian ta bi diddikin wannan kudiri da ke gaban ‘Yan majalisar jihar Kano, inda ta duba yadda kudirin zai shafi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II. Mun kawo yadda dokar za ta yi aiki.

1. Damar nada Majalisar Sarki da Mai Martaba Sarki

A wannan sabon kudiri, ana so doka ta karawa gwamna girma ta yadda zai zama shi ne mai ikon nada Sarki, kuma ya kafa Majalisar Sarkin. A baya, hurumin da aka ba gwamna shi ne ikon amincewa da matakin da Majalisar Sarki ta dauka a game da wanda zai hau kan gadon sarauta.

2. Amincewa da kasafin kudin Masarauta

Sashe na 25 na wannan kudiri zai taba Mai Martaba Sarki Muhammadu Sanusi, bisa dukkan alamu. Idan wannan kudirin ya zama doka, dole a duk karshen shekara kowace Masarauta ta gabatar da kasafin kudinta a gaban gwamna domin ya amince da kudin da za a kashe a fada.

3. Ragewa Sarakuna matsayi

A cewar sashe na 12 na wannan sabon kudiri, gwamna zai samu damar ragewa Sarki mataki ko kuma ya kara masa. Doka za ta ba gwamna ikon cewa wannan Sarki ya na daraja ta farko ko kuma ta biyu ko ta uku. A baya, Ganduje ya ba Sarakunan da ya nada matsayin matakin farko.

4. Tsige Sarki daga kan karaga

Sarki na iya barin kujerarsa idan ya ki halartar taron majalisar Sarakuna. Majalisar za ta kunshi Sarakuna 5 na kasar; Sakataren gwamnatin jiha, Kwamishinan kananan hukumomi, Shugabannnin kananan hukumomi 5, Mutum 10 masu nada Sarki, da Limamai, da wasu Wakilai.

5. Hana Mai Martaba Sarki magana

Wani bangare na sashe na 6 na wannan kudiri da ke gaban majalisa zai haramtawa Sarki fitowa bainar jama’a ya na ba gwamna shawara. Idan wannan kudiri ya samu karbuwa, Sarki bai isa ya soki gwamnati a fili ba, sai dai idan an bukaci ya bada shawarar da za ta taimaki jihar Kano.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button