Rayuwar wani direba Emmanuel Tuloe, ta Kyautata bayan ya tsinci Naira miliyan N25,000,000 kuma ya mayarwa da mai su
Emmanuel Tuloe, matashi ne dan shekara 19, wanda ya bar karatutun yana matakin furamare, a sakamakon rashin gata, yanzu yana karatu a makarantar ‘yayan masu kudi, da ba ma kowanne mai gatan yake samun shigar ta ba.
A shekarar da ta gabata, Emmanuel din yana ta gwagwarmayar yadda zai rufawa kansa asiri ta hanyar neman na kansa, sai ya tsinci wasu kudade a jakar leda a bakin titi, lokacin da yake aikin motar haya ta Tasi.
Ya sha caccaka da zolaya daga abokansa, wasu har cewa suke yi zai mutu cikin talauci, amma shi bai damu ba, wanda daga baya kuma wannan kyakkyawar Halayyar ta jawo masa alkhairai masu yawa.
Abu na farko da ya fara samu, shine yabo daga bangarori da dama, sannan wata makaranta mai suna Ricks Institute, dake kasar ta Liberia, wadda ta yayan masu hali ce, ta bashi gurbin karatu kyauta.
Bugu da kari, shugaban kasar Liberia George Wear, ya baiwa Emmanuel din kyautar dala dubu goma, $10,000,000. Ina da shima mai gidan rediyon da ya kai kudaden, ya bashi wasu kudade masu yawa. Shi kuma wani mai kudi ya bashi dala $1,500 duka kyauta.
Mafi mahimmanci a duk kyautar da ya samu, shine wata jami’ar kasar Amurka da ta bashi gurbin karatu kyauta bayan ya kammala sakandaren da yake yi.
“Ina jin ` makarantar da nake, ba wai don ta yi suna ba, a’a kawai saboda kyakkyawan horo da tarbiyya da ake bayarwa a fannin koyon ilimi, ” In ji Emmanuel
Da yake Emmanuel ya bar makaranta tun yana dan shekara 9, hakan yasa bashi da kyakkyawan asasi, wato fandisho, dalilin da yasa malaman suka yi masa wani tsari na musamman. kamar yadda wani malami mai suna Tamba Bangarori, ya shaida wa BBC.
Zama mutumin kirki abune mai kyau
Emmanuel ya kara da cewa:
” ya godewa Allah saboda damar da ya bashi ta aikata abin da ya dace, haka kuma ya godewa iyayen sa saboda tarayyar da suka bashi “
Kudaden da ya tsinta dalolin Amurka ne kimanin $50,000 wanda yayi daidai da kudaden Najeriya, Naira miliyan ashirin da biyar N25,000,000 tare da wasu kudaden kasar Liberia.
Emmanuel Tuloe, wanda ya tsinci miliyan 25m kuma ya mayar dasu ga mai su
A wancan lokaci, Emmanuel shine mai wuka da nama akan kudin, domin zai iya yin komai dasu ba tare da kowa ya sa masa ido ba, tunda babu wanda ya san ya tsinta, amma sai ya yanke shawarar ya kaiwa wata yar uwarsa ta ajiye kudaden.
Bayan sun adana kudin sai yaji ana cikiyar kudin a gidan radiyo, inda baiyi watawata ba, ya dauki kudaden ya kaiwa mai su.