Addini

Ramadaniyyat: 1443 [4] Imani Kadai Ba zai Isa Ba – Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo

1. Rayuwar dan’adam ba a bakin komai take ba, idan ba ya da imani da ilimin sanin Allah. Idan imani da sanin Allah suka tattara a zuciyar mumini, to lalle ya sami daukaka da jin dadi na duniya da na lahira.

2. Duk kuwa wani mai imani da ya rasa ilimin da zai nisanta shi daga bin tafarkin Shaidan, to lalle yana kan hadarin fada wa cikin shubuhohin Shaidan da makircinsa. Idan kuwa bai yi a sannu ba, to zai kai shi zuwa ga kafirci bai ankara ba.

3. Ibn Taimiyya yana cewa:

“Akan iya bai wa mutum imani tare da karancin iliminsa. To amma yakan iya rasa irin wannan imanin a koyaushe, kamar imanin Banu Isra’ila yayin da suka ga dan maraki. Amma wanda ya samu imani tare da ilimin sanin Allah, to wannan da wahala ya rasa imaninsa. Irin wannan mutum yana da wuya ya yi ridda ya bar Musulunci. Sabanin mai tsurar ilimi ko makarancin Alkur’ani ba tare da ya samu ilimin sanin Allah ba, to wannan da sauki yakan iya rasa imaninsa. Wannan shi ne abin da yake faruwa.

4. Yawancin masu yin ridda su ne makaranta Alkur’ani ba tare da suna da ilimin shari’a ba, wadanda kuma suka rasa imani a zukatansu. Ko kuma masu imani a zukatansu amma ba su da ilimin shari’a da na Alkur’ani.

5. Don haka, duk wanda yake da imani da ilimin sharia’r Allah da karatun Alkur’ani, to wannan ba zai rasa su ba a kirjinsa”. [Duba, Ibn Taimiyya, Majmu’ul Fatawa, Juzu’i na 18, shafi, 305].

6. Saboda haka, imani shi kadai tsagoronsa ba zai samu tsayawa kyam ba, sai ya hada da ilimin shari’a mai tushe.

7. Sau tari mutanen kirki da dama sukan kauce wa tafarki na gaskiya, ko kuma daliban ilimi da malamai sukan bar tafarkin Allah su kama na Shaidan, sai ka ga sun samu tangarda a addinisu.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button