Labarai

A Yi Watsi Da Batun Kidayar Jama’a A Magance Matsalar Tsaro — Kanal Dangiwa

Kanal Abubakar Dangiwa Umar mai ritaya, ya bukaci gwamnatin tarayya da tayi watsi da batun kidaya da za ta gudanar a shekara mai zuwa ta mai da hankali kan rashin tsaro.

Gwamnatin ta shelanta yin kidayar ce a jiya Alhamis a taron majalisar zartaswa da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci zamanta a fadar Gwamnatin a villa Abuja.

Jaridar Leadership hausa na ruwaito shugaban Hukumar ta Kidaya Alhaji Nasir Isa Kwara ya sanar da cewa, gwamnatin ta amince da a gudanar da kidayar a watan Afrilun 2023.

Ya ce, za a gudanar da aikin na gwaji a watan Yunin wannan shekarar bayan jam’iyyun siyasa sun kammla zabubbukan fidda gwani don fitar da ‘yan takararsu.

Ya kara da cewa, kidayar na da mahimmanci matuka domin ta hakane ake samun bayanai da za a gudanar da tsare-tsare don ciyar da kasa gaba.

Sai dai, a cikin sanarwar da Dangiwa ya fitar a yau Juma’a wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar hadin kai da cigaba (MUP) ya bukaci Buhari ya mayar da hankali kan batun kalubalen rashin tsaro da ke ci gaba da addabar kasar nan, inda ya yi nuni da cewa, a halin da Nijeriya ta ke a yau, maganar kidaya ba ta taso ba, kuma kidayar, barnatar da kudin kasa ne kawai.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button