Minista malami yace bazai ajiye muƙamin sa ba
Antoni-Janar na Ƙasa Abubakar Malami kuma Ministan Shari’a a ranar Alhamis yace bazai ajiye muƙamin sa ba.
Malami yace sai yaga ƙarshen wa’adin mulkin sa a watan Mayu na Shekarar 2023.
Malami ya bayyana haka, a lokacin da yake bada jawabin buɗe wa a wani taro, da Ƙungiyar Ma’aikatan Shari’a suka shirya.
Kamar yadda jaridar Jakadiyar RTV
“Mutane da dama da suka dogara ga jin bayanai na Ƙarya, suna cewa Malami ya ajiye muƙamin sa a Matsayin Antoni-Janar, kuma Ministan Shari’a, ana ganin sa a ofishin sa yana gudanar da aikace-aikace, ciki harda halartar taron Majalisar Zartaswa ta Ƙasa a jiya, kuma yanzu yana buɗe taro a matsayin Antoni-Janar na Kasa.
“Akwai ƙarshen komai. Wa’adina na Mulki har yanzu bai ƙare ba. Inda fatan inyi kyakkyawan ƙarshe,” inji shi.
Jita-jita na cigaba da yawo cewa Malami zaiyi takarar Kujerar Gwamnan Jahar Kebbi a Shekarar 2023, amma ɗan Shekaru 54 bai bayyana ra’ayin sa ba akan haka.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






MASHA ALLAH