Labarai

Jarumar fim tayi magana bayan bayyanar bidiyon tsiraicinta

Jarumar finafinan Nollywood, Empress Njamah, tayi magana a karon farko bayan bidiyon tsiraicin ta sun karaɗe yanar gizo.

Jarumar bata shiga sabuwar shekarat nan da kafar dama ba inda tsohon saurayin ta, Josh Wade, ya saki bidiyoyin tsiraicin ta ga ƴan midiya. Jaridar Daily Trust ta rahoto dimokuraɗiyyar na ruwaito

Njamah ta rabu da saurayin na ta inda ta bayyana cewa Wade yayi mata barazanar zai saki waɗannan bidiyoyin.

Jarumar fim tayi magana bayan bayyanar bidiyon tsiraicinta
Jarumar fim tayi magana bayan bayyanar bidiyon tsiraicinta

Wade ya tabbatar da barazanar da yake mata inda a farkon sabuwar shekarar nan ya buɗe wani dandali a WhatsApp inda ya sanya bidiyoyin jarumar da ya ɗauka a gidanta.

Hakan ya janyo kace-nace a kafafen sada zumunta, inda aka gargaɗi ƴanmata da su daina faɗawa irin wannan tarkon.

A wani bidiyo da jarumar ta fitar ranar Talata da daddare, tace duk matsalar da take fuskanta, tana godiya da har yanzu take numfashi.

Jarumar ta godewa masoyanta bisa nuna mata goyon baya inda tace da yawa daga cikin masu caccakarta ba su da masaniya kan haƙiƙanin yadda labarin yake.

Ina ƙaunar ku, ina cikin ƙoshin lafiya. Nagode sosai bisa ƙaunar ku, goyon bayan da saƙonnin ku da ziyarar ku. Ba za su iya ganin bayan mu ba. Mun fi ƙarfin dukkanin wasu shaiɗanu masu sharri.”

“Ina raye, ina raye har yanzu kuma ina da ƙwarin guiwar yin magana akai, mata da yawa ba su iya kaucewa wannan azabtarwar, wannan azabar, daga ƙarshe dai mun fi ƙarfin su. Ina matuƙar jin daɗin ƴancin da na samu.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button