Bidiyo : cikakken Bayyani Akan Sakin Aure A cikin Wasan Kwaikwayo ‘Film’ ~ Dr Bashir Aliyu Umar
Wata jaridar Intanet mai suna Fim Magazine sun yanko wani sashi na bayanin da Malaminmu Sheikh Dr. Bashir Aliyu Umar Hafizahullah yayi a cikin karatun Tafseer da yayi Mako uku da ya wuce, akan sakin aure cikin shirin fim.
Malam yayi bayani akan cewar duk wanda a cikin shirin fim yayi lafazin “NA SAKI MATATA” to matarsa ta zahiri ta saku. Su Fim Magazine ba su kawo cikakken bayani akan fatawar Malam ba.
Wannan yasa mutane da dama suke ta cece kuce akan batun. Gidajen Radiyo da na jaridu da yawa sun nemi karin bayani, ko son jin cikakken bayani kan wannan batu, musamman ganin cewar abin ya shafi celebrities.
Ga cikakkiyar fatawar da Malam yayi akan hakan, sannan shima Malam zai yi karin bayani akan abin da ya fada domin kaucewa kuskuren fahimta.
Ga bidiyon nan kasa ku saurara
View this post on Instagram