Labarai
Bidiyon budurwa tana rusa kuka akan saurayinta da suka yi shekaru 6 tare ya bar ta zai auri zabin mahaifiyar sa
Wata budurwa ta shiga cikin matsanancin tashin hankali kamar yadda ta bayyana a wani bidiyo tana rusa kuka.
A wani bidiyon TikTok wanda shafin LIB suka wallafa an ga budurwar cike da kunci har tana bayyana cewa shekarun su 6 tare da saurayin.
Ta ce yanzu haka ya yi danwaken zagaye zai aure wata budurwar ta daban wacce mahaifiyar sa ta zaba masa.labarunhausa na taƙaitomuna labarin
Ta ce shekarun su 6 suna soyayya cike da shauki amma duk da haka ya share ta zai sauya akalar soyayyar sa inda ya koma wurin wata daban.
Yanzu haka ta shiga damuwa saboda halin da ta tsinci kan ta duk da soyayyar da suka dade suna yi.
Ga bidiyon a kasa: