An Dauki Nauyin Karatun Budurwar Da Ta Fara Tattaki Daga Bauchi Zuwa Abuja A Kafa, Tare Da Bata Makudan Kudade
A yau Jumma’a Amira Ahmad ta hadu da dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi a Jam’iyyar APC Farouq Mustapha a gidanshi dake jihar Bauchi.
Idan baku manta ba, a jiya Alhamis “Daily News Hausa” muka kawo muku rahoton Amira Ahmad dake zaune a jihar Bauchi inda ta fara tattaki tun daga jihar Bauchi da niyyar zuwa Abuja domin nuna goyon bayan ta ga dan takarar Gwamnan Jihar a Jam’iyyar APC Farouq Mustapha, tare da karrama ‘yarshi kan namijin kokarin da tayi na shiga cikin tawagar talakawa a yayin taron Jam’iyyar da ya gudana a babban birnin Tarayya Abuja.
Dan takarar Gwamnan ya gaggauta dakatar da budurwar inda ya bada umurnin a dawo da ita gida duba da halin rashin tsaro da ake fama dashi, masu dakatar da itan, sun cimma ta a garin Jos suka dawo da ita gida.
A yau Jumma’a Amira ta hadu da dan takarar yayin ziyarar da ya kawo jihar Bauchi inda ya bata makudan kudade tare da daukan nauyin karatun ta baki daya.