Labarai

Jirgi na uku daga Saudiyya ɗauke da kayan agaji ya isa Beirut

Advertisment

Jirgi na uku daga Saudiyya ya isa Lebanon ɗauke da kayan agaji da suka haɗa da abinci da magunguna.

Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan da aka samu fashewar sinadarai a Beirut babban birnin ƙasar inda sama da mutum 150 suka mutu, kusan mutum 5,000 kuma suka jikkata.

Jaridar bbchausa ta ruwaito cewa jirigin ya isa Beirut kuma yana ɗauke da kayayyakin agaji da magungunan rage raɗaɗin ciwo da kuma na kashe ƙwayoyin cuta, da kayayyakin kariya da takunkumi da katifu da barguna da kayan kitchen da dai sauran kayayyaki.

Saudiyya na daga cikin ƙasashen da suka sha alwashin taimaka wa ƙasar ta Lebanon bayan afkuwar wannan lamari.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button