Labarai

Gwamnati za ta biya ASUU naira biliyan 30

Gwamnatin Najeriya ta amince ta biya ƙungiyar malaman ASUU kuɗaɗensu na alawus da ya kai naira biliyan 30.

Za a biya kuɗaɗen ne a rukuni biyu tsakanin Mayu 2021 da kuma Fabarairun 2022.

Jaridar Punch a Najeriya ta rawaito cewa gwamnati ta kuma amince ta kashe naira biliyan 20 wajen sake farfaɗo da ɓangaren ilimi wanda ke cikin buƙatun ASUU don kawo ƙarshen yajin aikin da yanzu aka shiga wata na 7.

Wannan na daga cikin yarjeniyoyi da gwamnatin ta cimma da Shugabannin ASUU a tattaunawarsu na daren Alhamis.

Kafin wannan lokacin ministan ƙwadago da ayyuka, Chris Ngige ya ce zaman gidan da ɗalibai suke yi ya taka rawa wajen hayar ɗalibai a zanga-zangar #EndSARS. Mun samu daga shafin bbchausa

Ministan ya ce yana fatan ASUU ta sanar da janye yajin aiki nan bada jimawa ba, sannan ya ce gwamnati nayin duk mai yiwuwa wajen ganin an daidaita, ɗalibai su koma makaranta.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button